Masu garkuwa da mutane da suka sace ma’aikatan wurin yawon bude ido na Kajuru a Jihar Kaduna bayan kashe wata Baturiya da wani sun bukaci a biya su Naira miliyan 60, kafin su sako ma’aikatan.
An sace ma’aikatan su uku ne a makon jiya, a yayin wani farmaki da aka kai a wurin yawon bude idon da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
Wata majiya, ta ce masu garkuwan ne da kansu suka kira daya daga cikin ma’aikatan wurin suka sanar da shi bukatar a biya su Naira miliyan 60 kafin su saki wadanda suka i garkuwa da su.
Wata ’yar Birtaniya, Faye Mooney, mai aiki da kungiyar agaji ta Mercy Corps Nigeria, na cikin mutum biyu da masu satar mutanen suka kashe a yayin farmakin, inda suka yi garkuwa da wadansu ma’aikatan wurin biyar.
Sai dai bayanai sun ce, biyu daga ciki sun tsere daga hannun masu satar mutanen, inda suka bar su rike da sauran mutum uku.
Wata majiya, a garin Kajuru ta ce, maharan sun yi kokarin kutsawa cikin harabar wurin shakatawar ne ta wani tsauni da ke daura da wurin shakatawar, inda suka bude wuta.
Majiyar ta ce, ’yan sanda biyu da ke gadin wurin sun yi kokarin mayar da martani, ta hanyar musayar wuta da ’yan bindigar, amma sai aka yi rashin sa’ a, ’yar Birtaniyar tare da wani abokin aikinta, suka razana inda yayin yunkurin sauka daga benen da suke kai ne suka gamu da harsashi.
A cewar majiyar, “Mutum biyu da aka kashe, sun shiga cikin dimuwa lokacin da suke cikin dakunansu a kan benen, sai suka yunkuro domin su tsira da ransu, yayin da suke kokarin sauka kasa, sai ’yan bindigar suka hango su, kasancewar kofofin benen a bude suke inda suka bude musu wuta.
Aminiya ta gano cewa wurin shakatawar na da nisan minti 15 ne kacal a mota daga Kasuwar Magani, inda aka yi ta samun barkewar tashin hankali a baya.
Idan dai ba a manta ba, a mako biyu da suka gabata, a wasu hare-hare da aka kaddamar kan kauyukan Banono da Unguwa Uku, a Karamar Hukumar Kajuru, ’yan bindiga sun hallaka mutum 20, tare da kone gidaje 10 da sace shanu 50.
Yunkurin jin ta bakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, a kan al’amarin ya ci tura.
Sai dai Ofishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda kungiyar da take yi wa aiki ta bayyana cewa sunanta Faye Mooney.
Kungiyar Mercy Corps ta ce Faye Mooney tana aiki ne a Najeriya, kuma abin takaicin ya faru ne a lokacin da wadansu ’yan bindiga suka far wa wurin da take hutunta a Jihar Kaduna.