Wadanda suka yi garkuwa da mutum biyar ’yan gida daya a yankin Kuje, Abuja, sun bukaci a basu miliyan N30 a matsayin kudin fansa kafin su sake su.
Aminiya ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ’yan uwan junan ne a ranar Talata da misalin karfe 11 na dare a rukunin gidaje na Pegi.
- An ceto mutum 9 da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Abuja
- Masu garkuwa da ma’aikatan Abuja na neman miliyan 110
“Mun samu mun yi magana da masu garkuwar a ranar Laraba, kuma sun bukaci a ba su miliyan N30 a matsayin kudin fansa”, inji wani makwabcinsu.
Ya shaida wa wakilinmu cewa masu garkuwar sun kira ne ta wayar mahaifiyar yaran da aka sace.
’Yan uwan da aka yi garkuwar da su su ne: Jibril Abdullateef mai shekara 22; Sherifat Abdullateef mai shekara 20; Muyidat Abdullateef mai shekara 13; Nura Abdullateefmai shekara 18; da kuma Na’imat Abdullatee mai shekara 9.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Abuja, Maryam Yusuf ba ta dauki waya ko rubutaccen sakon da aka aika mata ba, balle mu samu karin haske a kan halin da ake ciki.