✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa da kokunan kan mutane

An gano kokunan kan mutum da miyagun makamai a maboyarsu.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kogi ta cafke wasu mutum hudu a  kan zargin yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Kakakin Rundunar, DSP Williams Ayah ya ce an gano kokon kan mutum guda biyu da bindiga kirar gida guda daya da alburusai da sauran makamai a hannun wadanda ake zargin bayan an kama su a Karamar Hukumar Bassa ta jihar.

“Bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu da ake zargi da addabar Karamar Hukumar Bassa da kewayenta, jami’anmu sun kai samame wurin, inda suka shiga harabar gidan kuma suka cafke wadanda ake zargi,” inji shi.

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukan kuma za a mika su gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

“Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Idrisu Dauda Dabban, ya yaba wa namijin kokarin da ’yan sanda suke yi na yaki da bata-gari a fadin Jihar Kogi,” a cewar kakakin.