✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 14 a kauyukan Kaduna

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane akalla 14 a wasu kauyuka biyu a Kaduna cikin kwanaki biyu. Kauyukan da…

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane akalla 14 a wasu kauyuka biyu a Kaduna cikin kwanaki biyu.

Kauyukan da lamarin ya faru su ne Manini inda aka sace mutum 10 sai kuma kauyan Kwaru kusa da Labi akan hanyar zuwa Udawa inda aka sace mutum hudu.

A cewar daya daga cikin manyan ‘yan sintiri a yankin wanda bayasan a ambaci sunansa ya ce lamarin ya faru ne a ranakun Lahadi da Talatar nan da suka wuce.

‎Ya ce, dukka kauyukan da aka sace mutanen akan hanyar Birnin-Gari zuwa Kaduna ne. Amma dai kauyukan na a cikin karamar Hukumar Chikun ne.

” A yanzu akwai akalla mutum 14 a hannun masu garkuwa da mutanen wanda suka sace a wadannan kauyukun biyu. Daga cikin mutum hudu da aka sa ce akan hanyar Kwaru zuwa Labi akwai wata mai Sayar da abinci da ake kira ‘yar Kanawa sai kuma wani mai Suna Hamisu mai Awaki.

‎” Akwai wata tsohuwa mai Suna Yar Baki da wasu yara tagwaye Hasana da Husaina wadanda su an sallame su saboda kila basu iya sauri cikin daji. Ma’aikatanmu ne da suka bi sahun barayin suka tsinto su cikin daji,” in ji shi.

An yi Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo, amma abin ya ci tura domin layin wayarsa baya shiga.