Masu garkuwa da mutane ne a cikin daren jiya Litinin da misalin karfe 3 na safe suka yi awan gaba da wani babban jami’in lafiya a garin Dadin-kowa.
Ephraim Ajuji, Dan kimanin shekara 45 wanda kuma kwararre ne a aikin jinya da yake aiki a garin Dadin-kowa, masu garkuwan sun yi gaba da shi ne a Gidan sa da ke Unguwar Sarki a nan garin na Dadin-kowa.
Wata majiya ta shaidawa Aminiya, cewa masu garkuwan sun kwace dukkan wayoyin mutanen Gidan sannan suka sari daya daga cikin ‘ya’yan Ephraim din suka ji mata rauni.
Har ila yau majiyar tamu ta shaida mana cewa bayan masu garkuwan sun yi gaba da Ephraim da safen nan an ga motocin yan sanda na SARS Anti Robbery Squad suna ta shawagi a Unguwar.
Aminiya ta yi kokari dan jin ta bakin iyalan shi Ephraim Ajuji din amma lamarin ya faskara sai nan gaba idan hali ya yi za mu sake tuntubarsu.
..Suna neman miliyan 10 kudin fansa
Mary Ephraim mai shekara 18 Yar Mista Ephraim da ake garkuwa dashi ta shaidawa wakilinmu ta wayar salula cewa wadanda suka sake Babansu su nemi naira miliyan goma ko su kashe shi.
Mary ta ce a lokacin da mutanen suka shigo Gidan su sun buga musu kofa ne kan cewa su bude kofa da suka tambaya su wanene sai suka ce barayi ne suna budewa sai suka ga mutane da makammai da bindigogi irin na maharba da arduna har suka sareta akai.
A lokacin da za su tafi da babanmu sun kwace mana wayoyo guda uku na Mamar mu da nawa na Baban mu amma da suka zo tafiya sai suka ce idan suka tafi da wayoyin duka ba za su samu hanyar da za sunyi magana damu ba sai suka bar na Babanmu inji Mary.
Tace da misalin karfe bakwai na safiyar yau Talata ne mutane suka kira suka ce a basu naira miliyan goma ko su kashe shi amma tace su basu da wannan Kudin.
Zuwa lokacin aiko da wannan labarin dai iyalan ba su iya samar da wannan Kudi ba domin sunce basu da shi.
A bangaren yan sanda kuwa kwamishinan Yan sanda na Jihar Gombe Shino Olukola ya tabbatar da faruwar lamarin yace yan sanda suna nan sun shiga daji sai sun nemo wanda ake garkuwar dashi.