✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun gamu da ajalinsu a Ogun

An dauki lokaci ana artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta kashe wasu mutum biyu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a wani artabu a yankin Itori da ke gundumar Ewekoro ta jihar.

Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Litinin a garin Ota da ke jihar.

Oyeyemi ya ce da misalin karfe 7 na safiyar ranar Lahadi ne suka kai wani samame bayan da rundunar ta samu bayanan sirri cewar akwai masu garkuwa da mutane da ke boye a dajin da ke bayan Kwalejin Fasaha ta Otori,

Ya ce tuni jami’an fikira na rundunar aka aike su zuwa wajen da ake zargin ‘yan bindigar na boye sannan suka bankado su.

“Suna hango ‘yan sanda suka fara bude wuta, nan take jami’anmu suka mayar da martani kuma an dauki tsawon minti 40 ana dauki ba dadi.

“A yayin artabun ne aka kashe mutum biyu daga cikinsu yayin da ragowar suka tsere da raunukan harbin bindiga,” a cewarsa.

Kazalika, Oyeyemi ya ce an samu makamai da suka hada bindigu, wukake, harsasai da masu garkuwar suka gudu suka bari.

Ya kuma ce an samu wayar hannu guda biyu da kuma manyan jakukunan hannu guda biyu makare da kudade, sai takalman sawa.

Kwamishina ‘yan sandan jihar, Edward Ajogun ya jinjina wa jami’an jami’an kan namijin kokarin da suka yi na kawar da bata-garin.