Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da wasu masu ibada a Kauyen Maza-Kuka da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja, sun bukaci kayan abinci a matsayin fansa.
Daga cikin kayayyakin abinci da masu garkuwar suka bukata akwai katan-katan na lemun Maltina, jarkokin manja, buhunan shinkafa da sauran kayayyakin abinci daga ’yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su.
- Zaben Anambra: Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe guda 42
- APC ta yi Allah wadai da rikicin Gwamna Inuwa da Sanata Goje
Da fari masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa daga bisani sun nemi a basu Naira dubu dari biyu kacal da kuma lemun na Maltina, jarkokin man girki, shinkafa da sauran kayan abincin.
Wata majiya ta ce, “A ranar Juma’a ce aka kai musu Naira 200,000 da katan-katanna lemun Maltina da sauran kayayyakin abincin, amma sai suka rike mutane biyun da suka kai musu kayayyakin da cewar sun yi kadan.”
“Mun kashe akalla N50,000 wajen sayen kayayyakin abincin kadai, amma suka ce wai mun raina musu hankalin, kayan sun yi kadan” inji majiyar.
Kazalika, ita ma majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce har yanzu ba a sako ’yan uwan nasu ba, saboda an nemi sai sun sake kawo wata Naira 200,000 da kayan abinci.
Sai dai rundunar ’yan sandan Jihar ta ce ba huriminta ba ne yin sansancin biyan kudin fansa.
DSP Wasiu Abiodun, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, ya ce, “Mu ba ma goyon bayan biyan kudin fansa, ballanta mu shiga sansanci a lamarin.
“A yanzu haka dai muna iyakar kokarinmu domin ganin an ceto wadanda aka yi garkuwar da su.”
Idan za a iya tunawa, a ranar 25 ga watan Oktoba ne ’yan bindiga suka kashe masu ibada 18 a yayin da suke sallar Asuba a wani masallaci da ke kauyen Maza-Kuka da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama.