Rundunar ’yan sanda a Jihar Nasarawa ta tabbatar da sace Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Yakubu Lawal.
Aminiya ta gano cewa, wasu ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da Lawal a gidansa da ke Nasarawa Eggon hedikwatar Karamar Hukumar Nasarawa Eggon.
An samu rahoton cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.
Lamarin wanda ya faru a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, 2022, ya haifar da firgici a Karamar Hukumar Nasarawa Eggon, inda wasu ’yan bindiga suka kashe wani malamin makaranta a ranar Asabar.
An gano cewa, ’yan bindigar sun kai farmaki gidan Kwamishinan ne da misalin karfe 8:45 na dare inda suka yi ta harbi a iska don tsorata mazauna yankin kafin su yi awon gaba da shi.
Da yake tabbatar da yin garkuwa da Kwamishinan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Talata, Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan, DSP Rahman Nansel, ya ce tuni rundunar ta shirya jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru da nufin ceto wanda lamarin ya shafa.