Masu garkuwa da daliban makarantar Prince Academy da ke kauyan Damba-Kasaya a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun nemi a biya su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.
A ranar 17 ga watan Agusta ne ’yan bindiga suka dira garin da misalin karfe 8:30 na safe suka yi awon gaba dalibai biyar da ke karatu a shirinsu na fara jarabawar ’yan aji uku da malamarsu Christiana Madugu.
- Aminiya ta fahinci cewa, kudin fansar na dukkansu adaliban ne. Shugaban matasan yankin Akila Luka Barde ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigan sun kira iyayen yaran ne a ranar Asabar.
- Jama’ar gari sun cafke masu garkuwa da mutane a Katsina
- A karshe Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar Dadiyata
- ‘Yan bindiga sun tare hanya tare da yin garkuwa da mutane a Kano
“Eh, sun kira suna bukatar sai a ba su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa. Ni ban san a inda mutumin kauye zai samu irin wadannan makudan kudade ba. Amma dai muna ci gaba da yin du’o’i”, inji shi.
Ya kuma bayyana cewa, ana ci gaba da tattaunawa da ’yan bindigar domin a samu matsaya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mako daya ke nan da sace daliban amma Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumar ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Mohammed Jalige bai amsa wayarsa ba; Shi ma Kwamishinan Tsaro da Al’amurar Cikin Gida Samuel Aruwan bai amsa wayarsa ba, don samun karin bayani.