Shugaban kungiyar Masu dauke da Cutar kanjamau Ko Sida (HIb) reshen Jihar Yobe Alhaji Ali Baba Damaturu ya bayyana cewa suna samun sauki game da tsangwamar da kyamar da suke fuskanta daga al’umma sakamakon wata doka da gwamnatin jihar ta kafa kan hakan.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci mambobin kungiyar a ziyarar da suka kai wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Adamu Dala Dogo a ofishinsa da ke majalisar don nuna godiyarsa dangane kafa dokar hana tsangwama da kyamar da a baya ake nuna wa masu dauke da kwayar cutar.
Alhaji Baba Ali ya ce samar da wannan doka da aka yi ya taimaka matuka kan yadda a baya mambobin kungiyar ke fuskantar “cin zarafi da wulakanci iri-iri” a ofisoshi da gidajensu da sauran wuraren taruwar al’umma.
Daga nan ya yaba wa gwamnatin jihar dangane da yadda ta ware Naira miliyan 15 dangane da shirin kula da masu dauke da kwayar cutar kanjamau jihar.
A na shi bangaren, Shugaban Majalisar ya tabbatar wa mambobin kungiyar cewa a shirye suke na ci gaba da bai wa wannan dokar goyon baya da kuma goyon baya wajen ci gaba da tallafa musu da magungunan don kyautata rayuwarsu.
Masu dauke da Cutar kanjamau sun ziyarci Majalisar Jihar Yobe
Shugaban kungiyar Masu dauke da Cutar kanjamau Ko Sida (HIb) reshen Jihar Yobe Alhaji Ali Baba Damaturu ya bayyana cewa suna samun sauki game da…