✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu bai wa Gwamnatin Kano bashi su dakata —Abba Gida-Gida

Ganduje ya nemi Abba Gida-Gida ya dakata ya daina riga Malam masallaci.

Zababben Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi da cewa su dakata.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun zababben gwamnan, Sunusi Bature Dawaki Tofa ya fitar ranar Asabar.

Zababben gwamnan wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi na cikin gida da na waje da kada su amince da bai wa gwamnatin jihar bashi daga ranar 18 ga watan Maris zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, sabuwar gwamnatin ba za ta yi la’akari da bashin da jihar ta karba, ba tare da saninta ba daga ranar zabe zuwa ranar da aka rantsar da sabuwar gwamnatin.

Haka kuma, sanarwar ta ce masu bin gwamnatin jihar bashi a yanzu su kwana da sanin cewa za a sake nazarin ka’idojin bashin bayan kammala bincike a kan kowanne bashi da ake bin jihar.

Ana iya tuna cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce zababben gwamnan ya bayar da shawara ga masu gine-gine a filayen gwamantin jihar da su dakatar da ayyukansu nan take.

To sai dai bayan shawarar zababben gwamnan, gwamnan jihar mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar masa da martani, yana mai cewa sabon gwamnan ya daina riga Malam masallaci.

Ganduje ya tunatar da sabon zababben gwamnan cewa har yanzu shi ne mai iko da Jihar Kano, don haka ya yi hakuri ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.

A sanarwar da kwamshinan yada labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar ta ce abin da zababben gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, a daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu yake kan mulki, tamkar riga mallam masallaci ne.

A cewarta, “irin wannan shawara za ta iya haddasa rudani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.

Ta kara da cewa kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.