✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masoya Buhari ku yi soyayya don Allah

Abin da ya sa na ce masoya Buhari ku yi soyayya don Allah shi ne, akasarinku masoya Buhari kuna yi masa makauniyar soyayya, ta yadda…

Abin da ya sa na ce masoya Buhari ku yi soyayya don Allah shi ne, akasarinku masoya Buhari kuna yi masa makauniyar soyayya, ta yadda ba kwa iya gane kuskuren wanda kuke so, don haka makauniyar soyayya tana da alaka da shaidanci, saboda tana dauke da son zuciya. 

Ku bude idanuwanku domin ganin daidai da kuma kuskure, domin iya tantancewa tsakanin aya da tsaba, abin da ya sa na ce ku bude idanuwanku shi ne, domin ku kauce wa makauniyar soyayya ta yadda za ku rika fahimtar daidai da kuskuren da masoyinku yake aikatawa, a duk lokacin da ya yi daidai sai ku yaba masa, idan kuma ya yi kuskure, to ku kaunaci Allah ku yarda ya yi kuskure tun da shi ba Annabi ba ne, kuma ku nusashsheshi kuskurensa domin ya gyara, wannan ita ce soyayya mai idanu, kuma ita ce soyayya don Allah. 

Yana daga cikin matsalar rashin gina soyayya domin Allah, karshen abin ba zai yi kyawu ba ne kuma za a yi rabuwar baram-baram, yayin da ita kuma soyayya domin Allah ta kunshi alfanu da yawa, kuma har ma’aikin Allah ya ce “Akwai wadansu mutane bakwai da za su shiga inuwar al’arshin Allah ranar da babu wata inuwa sai ita,” to a cikin mutane bakwai din nan, akwai masu soyayya domin Allah.

Don haka yarda da cewa masoyinka ya yi kuskure a lokacin da ya yi kuskuren, kuma ka nusashsheshi kuskuren nasa domin ya gyara a nan gaba, shi ne soyayya don Allah, amma kin yarda da cewa masoyinka yanayin kuskure, ballantana idan ya yi kuskure ka iya fahimtar cewa kuskure ne har ka nusashsheshi domin ya gyara, to wannan ita ce makauniyar soyayya, wacce take kai mutum ga shaidanci, daga karshe mutum ya shiga halaka. 

AllahShi ne mafi sani…