✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masari zai gwangwaje zakaran gasar fasaha ta Katsina da kyautar mota

Ana sa ran rufe gasar ranar 15 ga watan Fabrairun 2022.

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, zai bayar da kyautar mota ga duk wanda ya zama zakara a gasar fikira da fasaha da ake dab da kammalawa a Jihar.

Kwamishinan Yada Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu na Jihar, Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika ne ya shaida wa wani taron manema labarai hakan a Katsina ranar Lahadi.

Kwamishinan yace, “Babban makasudin shirya gasar shi ne kirkire-kirkire da bunkasa hazakar matasan Jihar Katsina musamman, da na Najeriya baki daya.”

Kimanin ’yan takara 7,000 ne suka gabatar da sunayensu don gudanar da gasar da kuma atisayen tantancewa kafin daga karshe a zabo ’yan takara 250 bayan wani tsari mai cike da fafatawa.

An dai bajekolin kayayyakin da hazikan matasa 250 suka samar a lokacin da ake gudanar da atisayen gabatarwa a dakin taro na Cibiyar Gudanarwa ta Jihar Katsina, daga watan Nuwamba zuwa Disamban 2021.

An ware nau’ukan kirkira da fasaha don samar da mutane uku wadanda zasu yi nasara daga cikin rukuni hudu da aka kebe don gasar na zane-zane da samfuran motoci da fasahar sadarwa da kuma bangaren nishadi.

Tsarin kyaututtukan da za a bayar

Wanda ya zama zakara gaba daya za a ba shi kyautar babbar mota kirar Toyota High Lander Jeep wadda Gwamnan Jihar zai bayar.

Haka kuma, za a ba da kyautuka uku ga wadanda suka yi nasara a kowane rukuni daga cikin hudun kamar haka:

Za a baiwa wanda ya zama na farko kyautar Naira miliyan biyar, miliyan uku ga na biyu da kuma miliyan daya da rabi ga na uku.

Bugu da kari, ’yan takara 100 za a ba su
kyautar N100,000 kowanne a matsayin tukwicin shiga gasar.

Ana dai sa ran halartar muhimman baki daga ciki da wajen Jihar yayin gagarumin taron ba da kyaututtukan wanda za a gudanar ranar Talata, 15 fa watan Fabrairun 2022.