Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya gana da shugabannin Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) kan karancin man fetur da ake fama da shi a jihar da ma kasa baki daya.
Bayan kammala zaman a ranar Laraba, gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa taron wani yunkuri ne na ganin an magance matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a jihar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Takara Ke Kashe Kudi A Lokacin Zabe
- Yadda ’yan Boko Haram da ISWAP suka kashe juna a Borno
“Sun bayyana mana wani bangare na matsalarsu shi ce NNPC da ke karbar N172 da N174 kan kowace lita daga Legas.
“Amma ba a samun man fetur a Legas, don haka sai da suka koma saye daga masu shigo da kaya masu zaman kansu.
“Kuma masu shigo da kaya masu zaman kansu suna sayar da shi tsakanin N300 zuwa N310.
“Kuma idan wani ya yi jigilar wannan man daga Legas zuwa Katsina, akalla kowace lita na iya jawo karin N10 zuwa N20 na kudin sufuri. Kuma su ma sun san halin tituna ke ciki.
“Wannan batu ne da muka kai rahoto ga NNPC, kuma a yanzu mun samu jerin sunayen dukkan kason da aka ware wa Jihar Katsina,” in ji gwamnan.
Gwamna Masari, ya ce ga duk ’yan kasuwa masu zaman kansu da ke da matsala, “Ina rubuta wa sashen da abin ya shafa ne domin a magance wasu matsalolin, wadanda suka dade da biyan kudinsu a ba su kayansu.
“Kazalika, muna da ’yan kasuwa masu zaman kansu da ba su yi rajista da NNPC ba, saboda yadda tsarin yin rajistar yake.
“Mu a matsayinmu na gwamnati za mu taimaka musu don ganin sun yi musu rijista,” in ji gwamnan.
Wannan na zuwa ne bayan wahala da ake ta fama da ita a fadin Najeriya game da karancin man fetur wadda ta ki ci ta ki cinyewa.