Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya sanar da soke hawan Sallah babba kamar yadda aka tsara da farko.
Sarkin ya ce an soke hawan ne saboda shawarwarin mahukunta da masana kiwon lafiya kan annobar cutar Coronavirus da ke ci gaba da yi wa kasashen duniya barazana.
A madadin haka ne Sarkin ya nemi jama’a su yi amfani da wannan dama wurin gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya a Najeriya.
Ya kuma yi godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna saboda ayyukan da take gudanarwa a Zariya.
Haka kuma, ya yi kira ga gwamnatin ta himmatu wurin kammala aikin ruwa da ake yi a Zariya domin wadata jama’a da ruwan sha da kuma amfanin yau da kullum.
Kazalika, Sarki Bamalli ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba halin da jama’a ke ciki na kunci da tsadar rayuwa duk da cewa ana kokari, amma dai a kara saboda al’umma su samu sauki.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su dakatar da bukukuwan hawan Sallah Babba domin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin yaki da annobar a Najeriya, Boss Mustapha ne ya fitar da sanarwar ranar Lahadi a Abuja, Birnin Tarayya.
Matakin hakan dai ya biyo bayan sanya jihohi shida da kuma birnin Abuja cikin shirin ko-ta-kwana a wani mataki na dakile yaduwar coronavirus.
A halin yanzu dai kwararru kan sha’anin lafiya na gargadin yiwuwar sake barkewar annobar a karo na uku muddin ba a dauki matakan da suka dace ba.