✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Sarkin Hausawan Ibadan zata yi wa Hakimanta garanbawul

Mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji (Dakta) Ahmad Zungeru, ya sha alwashin yi wa Hakimansa garanbawul biyo bayan koken da jama’ar garin su keyi na…

Mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji (Dakta) Ahmad Zungeru, ya sha alwashin yi wa Hakimansa garanbawul biyo bayan koken da jama’ar garin su keyi na rashin tabuka abin azo a gani da suke zargin Hakiman su 80 da shi.

A jawabin da Sarkin Hausawan Ibadan ya gabatar a taron ci gaban al’ummar Hausawan Sabo Ibada da yammacin yau, Dakta Zungeru ya shaida cewa, kaso mafi yawa a cikin hakiman fadarsa basu san junan su ba, domin basa shirya tarukan ci gaban jama’ar su a tsakanin su ya ce wannan na cikin abubuwan da ke janyo koma baya tsakanin Hausawa a garin Ibadan.

Aminiya ta zanta da Sarkin Hausawan jimkadan da kammala taron inda ya shaida cewa, an kafa kwamitin mutum 10 da za suyi aikin tantance hakiman nasa, “Kasan wannan tsari ne na sarautar gargajiya ba na gwamnati ba, idan ‘yan kwamitin sun kammala aikin su zasu kafe sunaye duk Hakimin da bai ga sunan sa ba an kore shi kenan, sai dai amma ya iya nema a nan gaba idan ya gyara.” in ji Sarkin Hausawan Ibadan.

Kungiyar Garin Nagarke ce ta shirya taro domin lalubo bakin zaren ci gaban al’umar Hausawan Sabo Ibadan, taron da ya sami halartar ‘yan asalin yankin daga sassa daban daban na kasar nan.