Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sake nada wasu sababbni hakimai guda hudu tare da daga darajar wasu hakiman masarautar guda shida.
Da yake jawabi jim kadan bayan nada Hakiman, Sarki Aminu Ado Bayero ya ce an nada su ne bisa cancanta da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.
- Muna kokarin ceto yara da matan da aka sace a Zamfara —’Yan sanda
- Yadda ’yan ta’adda suka sace yara da mata 100 a Ramadan a Zamfara
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aiko wa Aminiya.
Wadanda aka nada din sun hadar da:
- Alhaji Nura Sunusi — Dan Darman Kano
- Alhaji Sarki Hamidu Bayero — Barayan Kano
- Alhaji Sayyadi Muhammad Yola — Fagacin Kano
- Alhaji Bello Idi — Kaigaman Kano.
Sai kuma Hakiman da aka daga darajanta:
- Malam Umar Sunusi Bunun Kano wanda ya zama Dan Makwayyon Kano
- Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano
- Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.