Mai Martaba Sarkin Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, ya soke gudanar da bukukuwan sallah da bisa al’ada aka saba gudanarwa a duk lokacin sallah.
Wannan mataki na zuwa ne bayan manyan masarautu a wasu jihohin kasar sun soke hawan sallah sakamakon fargabar barkewar annobar Coronavirus karo na uku da mahukuntan lafiya suka bayyana.
Sarkin, ya yi wannan kira ne a ranar Litinin cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai.
A cewar sakon da takardar ta kunsa, daukar matakin ya zama wajibi don taimakawa wajen dakile yaduwar cutar Covid-19 a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.
Mai Martaba Sarkin Jama’a ya bukaci jama’arsa da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga hukumomi kamar yadda aka sansu da yi, inda ya yi fatan kawo karshen wannan annoba da ta zame wa duniya alakakai.
Baya ga yi wa al’ummar musulmi na duniya fatan yin sallah lafiya, Sarkin ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna da jami’an tsaro musamman na ‘Operation Safe Haven’ da na ‘yan sandan sintiri na yankin da ke aiki ba dare ba rana wajen kwantar da duk wata barazana da wasu marasa son zaman lafiya ke kokarin tayarwa a yankin masarautar da kewayenta.
Kazalika, ya yi kira ga kowane bangare da su rika kai kokensu ga mahukunta a duk lokacin da suka ga wani abun da basu yarda da shi ba madadin daukar doka a hannu.
Aminiya ta ruwaito cewa, a kan gudanar da bukukuwan sallah ne a masarautar Jama’a da ke cikin garin Kafanchan ta hanyar zagaya manyan titunan garin jim kadan bayan idar da sallar idi.
Sannan washegari a kan gudanar da hawan daushe inda Sarkin kan kewaya babban titin garin zuwa Babban Asibitin garin inda ya kan ziyarci marasa lafiya tare da yi musu addu’a sannan ya basu gudummawa.
Daga nan kuma Sarkin ya kan gana da shugabannin asibitin inda suke mika irin nasu koke-koken da neman irin gudummawar da masarautar za ta iya bayarwa don ci gaban asibitin.
Ana iya tuna cewa, Masarautar Zazzau karkashin ta soke hawan sallah a bana.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Mai Martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna ya fitar a fadarsa a ranar Litinin.