✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Gwantu ta nada hakimai biyu

Mai martaba Sarkin Gwantu da ke Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, Birgediya Janar Iliya Yamma  ya nada hakimai biyu a ranar Asabar 15 ga…

Mai martaba Sarkin Gwantu da ke Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, Birgediya Janar Iliya Yamma  ya nada hakimai biyu a ranar Asabar 15 ga Disamban nan.

Bikin nadin wanda ya gudanar a fadar Etum Gwantu ya samu halartar mutane da dama.

Lokacin da yake jawabi jim kadan bayan kammala nadin, Sarkin ya hori hakiman su yi kokari wajen shawo kan kalubalen da ke yankunansu don dorewar zaman lafiya.

Sarkin ya umarce su da su yi biyayya ga na sama da su sannan su yi adalci ga talakawansu.

A lokacin da yake nasa jawabin, Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Al-Makura wanda mataimakinsa ya wakilta ya bayyana kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin jihohin biyu inda ya kara da yin kira ga hakiman da su karbi wannan nauyi da ya hau kansu da muhimmanci.

Yayin mai da jawabin hakiman da aka nada, Alhaji Bashir Mohammed (Hakimin Gwantu) da Rabaran Joel Galadima (Hakimin Fadan Karshi) sun mika godiyarsu ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i da Etum na Gwantu kan ganin cancantarsu da su ka yi wajen zabo su da dora musu nauyin shugabantar al’ummarsu inda suka yi alkawarin gudanar da mulkinsu cikin adalci ba tare da nuna bambamci ba.

Masarautu uku ne masu cin gashin kansu a Karamar Hukumar Sanga da suka hada da Gwantu da Fadar Ayu da kuma Fadar Ninzo.