Masarautar Borno ta samo asali ne daga tsohuwar Daular Borno wadda ta shafe fiye da shekara dubu da kafuwa. Wakilanmu sun tattauna da Dokta Musa Liman, Zannah Sobnoma na Borno inda ya bayyana yadda daular ta samo asali da irin sarakunanta da sauransu:
Mene ne takaitaccen tarihin Masarautar Kanem Borno.
Masarautar Kanem Borno masarauta ce mai dimbin tarihi don yau da kafuwarta ta kai sama da shekara dubu daya, asalin al’ummar Kanuri sun taho ne daga kasar Yemen.
Idan aka ce Kanuri kalmar daga Kannur take, domin Manzo (SAW), ya zo da addinin Musulunci, kabilar Kanuri da Shuwa su suka fara karbar addinin Musulunci, ma’anar Kannur yana nuna; nufin “Nur” wato haske“Nurul Islama,” masu haske da suka karbi addinin Musulunci babu ko tantama, shi kuwa sunan Borno ya samo asali ne daga “Baharnoor,” shi ne Baharmaliya, to asali a nan muka taso, kuma muka mika wuya tun farkon lamari.
To ita wannan daula ta fara ne tun daga can wajen birnin Digirni, sai ta fado can wajen Dahomi, sannan ta biyo har zuwa wajen Habasha da Nijar da Kamaru da Chadi, har ta gangaro zuwa Jamhuriyar Benin, duk wadannan kasashe a karkashin Daular Borno suke, domin daular ba karama ba ce tana da dimbin tarihi fiye da Daular Usmanu Dan Fodiyo ta Sakkwato.
Domin Shehu Usmanu Dan Fodiyo da ya zo jihadi ma ya tarar da Daular Borno kuma tana rike da addinin Musulunci wato a zaman kasa ce ta Musulmi shi ya sa bai yake ta ba. Tarihi ya nuna a cikin manyan Sahabban Manzon Allah, (SAW), wato Sayyidina Usman da Sayyidina Aliyu, suma sun taba zuwa Daular Borno, sun zo kasar Chadi da Kanem Mawo, kuma sun gangaro har Borno, to a takaice dai tarihin Daular Kanem Borno, yana da yawa kuma ya haura shekara dubu 1 da kafuwa.
Sarakuna nawa suka mulki Daular Kanem Borno?
To akwai nau’o’in sarakuna a wannan daular har kashi 2, wato akwai “Mai” su ne rukunin sarakuna na farko da suka fara sarautar Daular Borno sun yi sarakuna fiye da 30, sun riga sarakunan “EL-Kanemi,” ana cewa Mai Ari Gajimi, su Mai Idris Aloouma da sauran Mai din da suke cikin sarautar Mai suna da dama, kuma sun zauna a birnin Ngazargamu da birnin Ubojime da kuma birnin Saifawa.
To a lokacin nan su Kanurin sun rike addinin Musulunci amma ba su rike shi bisa ga Sunnar Manzon Allah (SAW) ba, sai Shehu Muhammad Al-Amin EL-Kanemi, wanda shi babban malami ne na addinin Musulunci, kuma shi ne Kakan- Kakan, Shehu na yanzu, ya zo da yaki domin kawar da dukkan wani nau’i na bidi’o’i da ake yi wadanda suka saba wa Sunnar Manzo Allah (SAW), har ya kai ga yakar Rabe ya kashe shi, kuma ya kafa Daular Shari’a irin ta Musulunci.
Shi ya canja wa sarautar suna daga Mai ta koma Shehu wato Shehun Musulunci daga malanta sai ya zama sarki amma sunan yana nan a (Shehu) wato Shehin Malami ga shi Sarki kuma Alkali wanda yake hukunci da Shari’ar Musulunci.
Tun daga kansa ya zama duk Shehun da zai zama Sarki ko kuma in ce Shehun Borno to ba zai zama ba har sai ya haddace Kur’ani da sanin Shari’ar Musulunci.
Daga cikin ’ya’yansa akwai su Shehu Umar Kura da Shehu Ibrahim da Shehu Darman da Shehu Hashimi da Shehu Ibrahim Masta Kura da Shehu Masta Kura, akwai kuma Shehu Masa Gana, to su dai wadannan su ne suka mulki Borno sun kai sarakuna 25, har zuwa kan Shehu na yanzu wato Shehu Abubakar Umar Ibn Garbai Al-Amin EL-Kanemi.
Shi kuma kakansa wato Shehu Abubakar Garbai takwaransa ke nan, shi ne ya kafa birnin Maiduguri a 1907, shi ne ya dauko hedikwatar daga garin Kukawa zuwa nan birnin Maiduguri, ya kuma gina wannan fadar Shehun da take a yanzu, zamani kuma ya zo aka yi ta yi mata gyare-gyare a gidan ana kawatawa.
Akwai Kur’ani Dubu a sama nan inda Shehu yake zama, wadanda Shehu Muhammad Al-Amin EL-Kanemi, ya rubuta ya kuma, ajiye a wurin. Shi kuma asalinsa mutumin kasar Sudan ne, domin iyayensa sun zo ne daga Yamen, har suka karaso Sudan a nan aka haife shi, kuma daga baya sai ya zo ya zauna a garin Ngala.
Kuma ana yi masa lakabi da Shehu Laminu-Dinai, wato ga shi malami kuma mai sarauta, Shehu na yanzu ya hau kujerar sarauta yau shekara 10 ke nan, kuma tun da ya hau sarauta alhamdulillahi, shi ya gaji yayansa marigayi Shehu Mustapha Umar EL-Kanemi, wanda ya yi shekara 35 yana mulki. Sai kuma baban Abubakar Shehu Garbai da kuma Shehu Umar Garbai wanda da Hakimin Maiduguri ne, to shi kuma ya hau gadon sarauta a 1967, shekara 6 ya yi a sarauta.
Sai Shehu Umar Sanda Shehu Kyarimi, shi kuma ya yi shekara 23 a garin Dikwa yana sarauta, sai Turawa suka yi masa canjin wajen aiki zuwa nan Maiduguri, ya zo ya sake shekara 29 a nan Maiduguri kuma a kan gadon sarauta wato ya kwashe shekara 52 yana mulkin Daular Kanem Borno.
Mai sun yi sarakuna za a iya cewa sun haura 30, har sun fi na EL-Kanemi yawa, don El-Kanemi sun yi sarakuna 25, to ka ga ke nan yawan sarakunan Daular Borno sun kai 60.
Da sarautar “Mai” da “El-Kanemi” su ne suka mulki Borno yawansu ya kai sarakuna 60 a cikin shekara fiye da dubu daya da masautar ta yi.
Shin akwai dangantaka ce a tsakanin gidajen sarautun biyu na Mai da Kanem,?
Za a iya cewar babu wata dangantaka a tsakanin gidan sarautar “Mai” da El-Kanem, domin su Mai, Saifawa ne, don sun yi shekaru da dama suna yi kafin ya fado hannun EL-Kanemi.
Shi kuma EL-kanami kamar yadda na fada mahaifinsa ba Sarki ba ne, kakansa ba Sarki ba ne malami ne, kawai shi ya zo ne da “Da’awa” kira zuwa addinin Musulunci ganin irin yadda abubuwa suka tabarbare duk da cewa akwai addinin amma ba a aiki da shi.
Mece ce ma’nar wannan sarauta ta “Zanna Sobnoma” kuma yaya aka yi aka samu kai a ciki?
Abu ne wanda ya zo ya hada da tarihin gida da gyaran lamura gami da rike al’adu, idan ya zo ya same ka ba za ka ki ba. Lokacin da Shehu ya kama mulki da farko cikin mutanen da ya kira Fada ya ce mana ku ne mutanen da za ku tafiyar mini da wannan mulki, a wannan lokacin ya ba ni Sarauta ta Zanna Sabnoma ma’ana shi ne “Mai gayyata,” kana daya daga cikin mutanen da za ku taimaka min.
ShekarA 40 da suka wuce muna tare da shi kuma mun yi makaranta tare da shi a firamare, duk da suna gabanmu da shekara daya, domin yayana Bashehu shi ne abokinsa, to ka ga idan ya kira ni ya ce in tallafa masa a kan wani abin da na san ci gaba ne musanmman ga Masarautar Borno to dole ne in karba don ci gaban al’ummarmu.
To sannan kuma tun lokacin muna yara muna wasanni irin na yara na gargajiya idan muna wasan Sarakuna da ire-irensu shi ne Shehunmu kuma ni ne Zanna, to haka dai muke ta wasanni ga shi kuma ya zo ya zama gaske kuma tarihi ya maimaita kansa, sai Allah ya sa muka zama abin da muke ta mafarki a kai, to aiki dai ba wani aiki ne mai wuya sosai ba, amma za a kuma iya cewa yana da wuya.
Ma’anar Zanna Sabnoma, a Hausance “Sarkin Gayya” ke nan duk taron da Mai martaba Shehu, zai yi ni ne zan tara mutane, amma fa akwai ZannaTarnoma shi kuma zai sallami mutane bayan an kammala taro, kuma wannan sarauta tamu tun zamanin Shehu El-Kanemi akwai ta, a yanzu an dada jaddada mana ita.
A karshe wane fata kake da shi ga al’umma da ita kanta Masarautar Borno?
Ni dai fatana ga al’ummar Masarautar Borno, ko da yake kafin nan Allah Ya jarabce mu da shiga wata masifa tun hawa karagar mulkin Mai martaba Shehu, na yanzu yau shekara 10 ke nan, ina so mutane su san cewa jarrabawa ce daga Ubangiji.
Domin tun hawan Shehu zuwa yau ba mu samu kwanciyar hankali kamar na da ba, kuma wannan ba wani camfi ba ne, wai a ce a lokacin kakanninsa Shehu Sanda, an yi irin wannan.
Allah ne dai Ya kawo mana, kuma Shi ne Mai zamani, to yanzu fatana Allah Ya kawo mana karshen wannan lamari, sannan mu ci gaba da hada kawunanmu, mu tura yaranmu zuwa makaranta.
Gwamnati kuma ta yi kokari ta samar wa matasa ayyukan yi, sannan mu dawo da al’adunmu da dabi’unmu kamar da.
Mu rika girmama iyaye da kuma sa ido a rayuwar ’ya’yanmu mu san da wadanda suke hulda.
Mu koma matsayinmu na da a san wane ne Bulama a san wane ne Lawani, a san wane ne Hakimi, wato a koma tsari irin na da a rika girmama masarautu.