Majalisar Masarautar Adamawa ta tube rawanin Hakimin Ribadu da ke Karamar Hukumar Fufore da ke jihar, Alhaji Gidado Abubakar.
Mukaddashin Sakataren masarautar, Alhaji Kabiru Bakari, na ya sanar da hakan a cikin wata takarda da ya aike wa tubabben hakimin.
- Ayyuka 10 da Abba Gida-Gida ya yi bayan hukuncin kotu
- Sarakunan Arewa mazauna Kudu sun yi watsi da batun dakatar da Sarkin Sasa
“Majalisar Masarautar Adamawa ta umarce ni da in rubuta in kuma sanar da kai cewa Gwamnan Jihar Adamawa ya amince da korar ka.
“Ka mika duk wasu takardun hukuma da ke hannunka, ciki har da takardar shaida, ga Mukaddashin Sakataren Masarautar Adamawa da ke Yola,’’ in ji wasikar.