✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masar ta fasa yin wasan sada zumunta da Najeriya

kasar Masar ta ce ta fasa yin wasan sada zumunta da ta shirya a tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.A da kasar ta…

kasar Masar ta ce ta fasa yin wasan sada zumunta da ta shirya a tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.
A da kasar ta shirya wasan ne a ranar 9 ga watan Janairun, 2017 a kasar Dubai a shirye-shiryen da Masar din take yi na tunkarar gasar cin kofin Nahiyar Afirka da zai gudana a Gabon kuma Najeriya ba ta cikin kasashen da za su fafata a gasar.
Masar ta ce ta soke wasan ne saboda ba za ta iya daukar dawainiyar ’yan kwallon kafa na Super Eagles hade da jami’ansu ba, da hakan ya sa ta karkata akalarta zuwa kasar Tunisiya da ke makwabtaka da ita don gudanar da wasan sada zumuntar.
Kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato cewa Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bukaci Masar ne da ta dauki nauyin daukacin ’yan kwallon Super Eagles da jami’ansu a sharadin yin wasan amma Masar ta ce hakan ba zai yiwuwa ba musamman a wannan lokaci da take fuskantar rashin kudi.
Sai dai Sakatare Janar na Hukumar NFF Mohammed Sanusi ya ce har lokacin hada wannan rahoto ba su samu wata takarda daga Masar da ta nuna ta soke wasan ba.
Masar dai tana son gudanar da wasan sada zumunta ne a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin Afirka da zai gudana a watan Janairun badi a kasar Gabon.