✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masar dankali

 Barkanmu da sake haduwa uwargida a cikin wannan fili na girke-girke. Tare da fatan ana lafiya kuma ana gwada duk nau’o’in girke-girke da muke kawo…

 Barkanmu da sake haduwa uwargida a cikin wannan fili na girke-girke. Tare da fatan ana lafiya kuma ana gwada duk nau’o’in girke-girke da muke kawo muku. A yau na kawo muku yadda ake hada masar dankali ce, a sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

• Dankali

•Attarugu

• Albasa

• kwai

•Gishiri da magi

• Kori

Hadi

Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta dora a wuta ya nuna ya yi luguf sosai. Sannan sai ta dauko roba ko kwano mai zurfi ta zuba a ciki. Sannan sai uwargida ta debo kwai ta fasa a kan dankalin. Sai ta samu ludayinta ta dama dankalin da kwan har sai sun hadu sosai. Sai ta debo albasa da attarugu ta jajjaga sannan ta zuba a kan hadin dankalin da magi da gishiri da kori daidai dandano sannan sai a sake dama hadin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.

Idan uwargida ta gama haka, sai ta dauko tanda ta dora a kan wuta. A zuba man gyada a kowace kusurwa sannan a debo kullun dankalin a zuba a kowace kusurwar tanda. Sannan sai a bari na mintuna kadan domin  hadin ya nuna. Idan gefe daya ya yi, sai a sake juya daya gefen har sai ya nuna sai a sauke.