Masana ilimin kimiyya sun gano wata karamar halitta a jikin wani dutse a Arewacin Australiya, wacce aka yi ittifakin ta shekara kimanin biliyan daya a doron kasa.
Binciken, a cewarsu, zai iya canza fahimtar da duniya take da ita a kan ainihin mutanen da suka fara zama a doron kasa.
- Kaduna: Abu 5 da Gwamna Uba Sani ya yi a kwana 10
- Wani mutum ya caka wa kananan yara 4 wuka a Faransa
Halittun, wadanda ba a iya gani sai da mudubin hangen nesa ana kiransu ne da Protosterol Biota, kuma dangi ne na halittun da ake kira da eukaryotes, wadanda suka rayu a doron kasa kimanin shekaru biliyan daya da miliyan 600 da suka gabata.
Irin halittun da suke da nasaba da halittun na eukaryotes a yanzu sun hada da funfuna da tsirrai da dabbobi da kuma halittu masu kwai guda daya irin su ‘amoeba’.
Mutane dai ana hasashen halittun da ke da nasaba da su sun fara zama a cikin wannan duniyar sama da shekara biliyan daya da miliyan 200 da suka gabata.
A cewar Benjamin Nettersheim, wanda ya kammala digirinsa na digirgir a Jami’ar Australiya, wanda yanzu haka yake Jami’ar Bremen da ke Jamus, ya ce, “sabon binciken ya nuna ainihin halittun da suka fara zama a duniya, tun ma kafin dan Adam.
“Wadannan halittun sun yi rayuwa sosai a cikin ruwa, kuma watakila suna da alaka sosai ta tarihi da halittun da suke rayuwa yanzu a doron kasa.”
Gano halittun ya biyo bayan shafe tsawon shekara 10 yana bincike a Jami’ar ta Australiya, wanda aka wallafa a mujallar Nature ranar Alhamis.