Sojojin Isra’ila sun kai wa masu sallar dare a Masallacin Kudus sabon hari a cikin kasa da kwana uku.
Akalla Palasdinawa 300 ne suka samu raunuka a sakamakon farmakin na ranar Litinin, wanda ke ta shan suka daga sassan Duniya.
Isra’ila ta kai wa masallatan sabon harin ne a yayin da aka kammala sallar dare a masallacin mai alfarma, suka kuma tsare su.
Farmakin na ’yan sandan Isra’ila a Masallacin Kudus ya haifar da zanga-zanga a Tel Aviv, babban kasar, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Rahotanni sun ce ana zaman dar-dar a yankin Zirin Gaza, inda hare-haren sama da Isra’ila ta kai suka jikkata akalla mutum 200.
Masu aikin ceto sun ce akwai yiwuwar karuwar wadanda suka jikkata, muddin ba a yi wa hare-haren linzami ba.
Tuni kasashe suka fara yi tofin Allah-tsine ga hare-haren na Isra’ila tar da jawo zanga-zanga a kasar Turkiyya.
An samu zanga-zanga da dauki ba dadi tsakanin Falasdinawa da dakarun gwamnatin Isra’ila wadda ta sanar da aniyarta ta mamaye yankunan Falasdinawan.
Bayan bayyana damuwarta game da hare-haren, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi zama da jakadan Isra’ila, amma bai fitar da wata sanarwa a kan lamarin ba.