✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masaka na bukatar tallafin gwamnati – Abdulhamid Masaki

Sana’ar saka kayan gargajiya sana’a ce mai dadadden tarihi. Wakilinmu a Kalaba ya yi tattaki zuwa garin Ogoja, Jihar Kurosriba inda ya zanta da Malam…

Sana’ar saka kayan gargajiya sana’a ce mai dadadden tarihi. Wakilinmu a Kalaba ya yi tattaki zuwa garin Ogoja, Jihar Kurosriba inda ya zanta da Malam Abdulhamid Ilya, wani masakin gargajiya da ya kware wajen saka zane Mudukare. A hirarsu da masakin ya ce suna bukatar gwamnati ta tallafa masu, su bunkasa sana’arsu, gudun kada sana’ar ta yi mutuwar tsaye. Ga yadda hirarsu ta kasance:

Ko Sana’ar saka ta kasu kashi nawa?
Saka ta kasu kashi biyu a gargajiyance, domin wannan ita muka fi yi. Farko akwai sakar fari sannan kuma akwai ta mudukare, ita ce wannan da ka iske ni ina yi. Mudukare zane ne da Fulani suke daurawa, mu ne muke saka masu shi.
Hala ka samu lokaci mai tsawom kana yenta, ko kuwa da rana tsaka ka kama yinta?
Na shafe shekara 20 ina yin wannan sana’a ta saka kuma gadonta na yi iyaye da kakanni. Amma da can kakanninmu ba irin wannan suke yi ba.
To wace iri suke yi?
Ta fari suke yi, wanda bai wuce tafin hannu ba, don haka za ka ji labarin wata saka wadda ake ce mata sakar fari, to da ita suke yi.
Canjin zamani ne ya sanya aka koma ta mudukare?
Eh, canjin zamani ne ya kawo haka sai muka samu matsefi babba ba kamar yadda a da can ake yi da karami ba. To shi ne sai muke yin zannuwa, shi ne ka ga abun ya zo a haka a yanzu.
Kamar idan mutum yana so ya zama masaki shi ma, da me-da me ake bukata na kayan aiki da za a tanada?
Yauwa, farko kamar idan mutum yana son ya fara wannan sana’a tamu, idan masaki yana son ya yi ta da farko zai tanadi zare tukun, idan ya sayo zare sai ya zo ya nemi allera sai kuma ya nemi matsefi irin wanda mutanenmu suke yi na gargajiya tun tuni. Bayan wannan, idan ka tanade su sai ka zo ka je ka nemo itace a dawa, sai ka zo ka gina ka kakkafa; ta zama masaka ke nan. Sai ka yi saitin ta, to shi ne sai ka zo ka zauna ka yi shirin hada ta amma ita dai farko ta fi son ka nemi matsefi mai kyau, ka nemi kuma fili; ba za ta yiwu ba idan ba a fili ba.
Kamar wadannan abubuwan da na ga kana jefawa hannunka na dama zuwa na hagu fa, yaya sunan sa?
Ita wannan da nake jefawa dama da hagu din nan, ita ce koshiya.
To, su kuma wadannan abubuwan da na ga kana tabawa yaya sunansu?
Wadannan abubuwa guda uku? Wadannan biyu na gaba su ne Allera wannan kuma na gabana da ake jawowa haka shi ne Matsefi, shi ke tace zaren kamar idan na jefa haka ai ka ga ya fita ko? Idan na jawo shi haka ka ga ya tace ta ko?
Shi kuma na kafarka fa, da na ga kana takawa, ya sunansa?
Yauwa, to shi kamar wannan na kafa da ka gani ake takawa shi ne ake ce wa Kalallabai. Shi wannan kalallabi da ake takawa, shi ne kamar inji, idan na taka dama zai bude idan ma na taka hagu zai bude.
Na ga zaren ma akwai fari akwai ratsin launin ja da kuma baki, an ja shi da tsawo, an nade shi kan wani dutse; shi kuma me ke nan?
Shi kuma sunansa kunkuru.
Daga cikin wannan da kake sakawa, na lura kana ratsa wani ado kamar fulawa, akwai launin baki akwai na ja, da kuma mai kama da ruwan goro. Shi kuma wace hikima ce ta kawata zanen ake yi?
Ka san idan za mu yi wannan, zaunawa muke yi a zaune mu shirya ta, idan muka shirya shi wannan da kake gani farin, to shi za mu fara sanyawa iya yawan zannuwan da ka shirya haka za ka rika ratsa su kamar ado. Duk kalar da ka sanya in baki in fari ko ja, haka zai fita shi ne ake nufin zane mudukare ke nan.
Na lura kana sanya wani karfe kana murda sakakken zuwa gabanka, shi kuma karfen mene ne sunansa da kuma hikimar yin hakan?
Wannan da ka gani ina nadewa, shi muke ce wa Takala. Idan ba shi wannan karfen, to zanen ba zai tsaya ba, dole ne muke sanya shi don idan mun jawo mun harde, zanen ba zai tafi ba, amfaninsa shi ne yake kara kyan sakar.
Akwai zane da ake kira Asiwoke, ko ku ma kuna saka irin wannan zanen?
A’a, mu a nan ma ba mu yin Asiwoke, mu a nan abin da muka fi yi sai dai mu yi fari, sai kuma mu yi wannan mudukare; shi muka fi yi a nan wajen.
Kamar su waye suka fi sayen wannan kaya idan kun saka?
Wani lokaci muna zuwa Kaduna mu sayar da kuma sauran manyan biranen kudu da na arewa. Wani lokacin ma muna sayarwa a nan garin, duk ba yadda kasuwa ba ta kamawa ko kai wa. To, amma akwai mutane na musamman da suke zuwa suna sayensu, wanda dama can su sana’arsu ke nan. Idan mun yi to sai su zo su saya a wurinmu. Su ne suke tafiya kudu da shi da kuma yamma suna bin wurin da Fulani suke suna sayarwa. Hatta mutane ma namu masu sha’awa, suna zuwa su saya. Fulani ma da idan suna da wata hidima ta biki, suna zuwa su saya.
Ka taba neman tallafi domin ka bunkasa sana’arka mataki a karamar hukuma ko gwamnatin jiharku?
Eh, to, a da can dai mun taba nema bayan da muka kafa kungiya ta masu sana’ar sakar kayan gargajiya, ni da wasu mutane na ruga, muka je neman tallafi. Abu dai ya shiririce shiru, mun yi, mun yi ba mu samu ba har ma dai muka ji haushi, mu kuma muka ki bi, ka san ita gwamnati ita idan ba bi ka yi ba, ba za fa ta tuna da kai ba; to shi ne muka ki bi balle ta tuna da mu.
Wato dai da haka abun ya sha ruwa?
Da haka dai abu ya shiririrce, kowa ya kama gabansa. To k aji dalilin da kungiyarmu ta lalace. To, amma a yanzu din nan idan gwamnati za ta shigo cikin wannan sana’a ta mu to za mu tsaya mu bunkasa ta mu adana ta yadda kowa zai kara sha’awarta tun da sana’a ce ta gargajiya.
Wane kalubale kake fuskanta a kan wannan sana’a taka?
kalubalen da nake fuskanta a wannan sana’a daya ne, farko idan mun je sayo zaren nan kamar yadda da muke sayo shi da dan sauki-sauki, to a halin yanzu ya yi tsada fiye da yadda ake za to, yanzu to shi ya sa shi ne yake ba mu wahala. Yanzu wajen hada kayan aikin nan kuma kamar yadda nake ce maka wannan shi ne Allera, wannan shi ne Matsefi ne, yanzu idan ba mutane irin na da ba, na yanzu ba za su iya hada ta ba sai dai yara. Yara kuwa yanzu ba za su iya hada ta ba, tun da ba su san yadda take ba, ka ga shi ma wannan yana kawo mana koma baya a kan sana’ar da muke yi.
Ya zuwa shekaru 20 da ka yi kana wannan sana’a, kwalliya kuwa na biyan kudin sabulu?
kwarai ma kuwa, kwarai kwalliya ta biya kudin sabulu tun da da abin da ba ni da shi kafin na fara saka da hidimar da ban yenta, yanzu da nake wannan sana’a babu abun da zan ce sai hamdala ga Allah. Na samu na kuma karu da ita sosai, shi ya sa ma ka ga na dage ina yinta.
Lura da sauyin zamani, cikin ’ya’yanka za ka so wani ya gaje ka?
kwarai ma kuwa, kwarai, idan ka ga dai cikin ’ya’yana wani bai gaje ni ba sai wani ikon Allah. Sai dai kuma da yake zamani ne ya zo kuma ga shi sakar yanzu ta zama ta zamani, to ga shi zamani ya zo, su yaran ba su son zama, yanzu duk wanda ka ce ya zo ya zauna ya ga ma yadda kake shiryata ma to ba fa zai zauna ba, balle ya ga yadda kake shirya ta.
Wane sako gare ka ga ’yan uwa masaka?
’Yan uwana masu sana’a irin tawa ta gargajiya din nan, sakon da zan yi masu shi ne, sai in ce su zo mu taru mu hada kai mu je mu nemi tallafi wurin gwamnati; domin bunkasa sana’armu. Idan abun zai yiwu, ko ma don kada a barta ma ta lalace.