Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta yi gargadi dangane da masu bukatar ganin an halasta shan tabar wiwi da kuma noma ta a cikin kasar.
Shugaban Hukumar, Janar Muhammad Buba Marwa ne ya bayyana haka yayin gabatar da jawabi wajen wani bikin da ya gudana ranar Juma’a a Akure.
Marwa ya ce yawan ’yan Najeriyar da ke busa tabar wiwi ya zarce yawan al’ummar kasar Portugal mai mutum miliyan 10 da dubu 100 ko Girka mai miliyan 10 da dubu 700 ko kuma Jamhuriyar Benin mai mutane miliyan 12 da dubu 100.
Tsohon gwamnan Lagos ya ce Najeriya ba ta da tsarin sanya ido a kan masu amfani da tabar wiwin kamar kasashen da suka ci gaba, saboda haka halasta ta zai yiwa kasar matukar illa.
A cewarsa, miyagun kwayoyi cikin su har da wiwi na matukar tasiri wajen aikata manyan laifuffuka a Najeriya, saboda haka yana da muhimmanci a hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalar.
Ya kuma yi gargadi a kan mutanen da suka mayar da tabar wiwi tamkar wata alawa lura da irin illar da take yiwa jama’a, yayin da ya bayyana aniyar hukumarsa na ci gaba da yaki da masu noma ta da kuma masu amfani da ita.