Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya ce jam’iyyar PDP ce ta kyankyashe Boko Haram a Najeriya.
Lai ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar, wanda ya ce ya kasa gane wa al’amarin Boko Haram a kasar.
- NAJERIYA A YAU: IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya?
- Amurka na neman kwace alakar kasuwancin China a Afirka
Ministan ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya shirya ranar Litinin a Abuja.
Ya shawarci tsohon Mataimakain Shugaban Kasar da ya daina nuna kamar bai san abin da ke faruwa ba game da matsalar Boko Haram da ta samo asali a 2009 a lokacin da jam’iyyarsa ta PDP ke rike da kasa.
A baya, an ji Atiku ya fada yayin wani taro cewa, ya kasa fahimtar al’amarin Boko Haram.
Dan takarar ya ce har yanzu an kasa shawo kan matsalar Boko Haram duk da kokarin da sojojin Najeriya ke yi wajen ganin bayanta.
Sai dai da yake mayar masa da martani, Minista Lai ya ce babu bukatar Atikun ya je da nisa kafin ya fahimci abin da ke faruwa.
Ya ce, ya je ya tambayi shugabancin jam’iyyarsu dalilin da ya sa suka bar Boko Haram ta ci karenta babu babbaka inda suka yi ta tada bama-bamai a garuruwa da makarantu da garejin motoci da sauransu.