✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani a kan Jigawa 2023: Wai mene ne zunubin Bahadeje ne?

Na karanta wani rubutu da jaridarku mai albarka ta Aminiya ta ranar 25 ga Fabrairun nan mai take da ke sama wanda Alhaji Ahmed Ilallah…

Na karanta wani rubutu da jaridarku mai albarka ta Aminiya ta ranar 25 ga Fabrairun nan mai take da ke sama wanda Alhaji Ahmed Ilallah ya rubuta.

Duk da yake marubucin ya fadi ra’ayinsa ne, amma kama sunaye da ya yi da misalan da ya yi kokarin kawowa ya sa ya zama dole in yi wannan rubutu domin wayar da kan dubban masu karatu da kuma yi wa tarihi adalci Da farko dai a matsayina na cikakken Bahadeje daga Karamar Hukumar KafinHausa ban taba jin cewa akwai wani yanayi na bambanci da ake nuna min a tafiyar siyasar Jihar Jigawa ba.

Hasali ma, sai dai in ce idan aka kwatanta da wasu yankunan na Jigawa, to mu Hadejawan a iya cewa kusan mun ci rabonmu mun fara shiga cikin na wadansu.

Zan koma tarihi don bin irin tagomashin da muka samu a wannan yanki tun dawowar dimokuradiyya sama da shekara 23 da suka wuce. Jigawa kamar kowace jiha kashi uku ne a bisa tsarin mulki na kasa; wato Arewa ta Tsakiya (Masarautar Dutse) da Arewa maso Yamma (masarautun Gumel da Kazaure da Ringim) da kuma Arewa maso Gabas (Masarautar Hadeja).

Kuma akwai kashe-kashe na tsarin masarautunmu masu albarka na Dutse da Hadeja da Gumel da Kazaure da kuma Ringim.

Alhamdulillah mu mutanen Hadeja muna yi wa Allah godiya sannan ’yan uwanmu mutanen Jigawa kan cewa a kowane tsagi mutum ya dauko wadannan rabe-rabe na Jigawa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Mu Hadejawa sai sam-barka idan aka dubi cewa mu ke jan ragamar harkokin tattalin arzikin Jihar Jigawa wanda galibinsa noma da kiwo da kamun kifi ne. Ga kuma albarkar karatu da shiga aikin gwamnati a tarayya da jiha da Allah Ya yarje (a wasu bangarorin) ’yan uwanmu na Jigawa.

Muna da babban birnin masarauta a Hadeja wanda ba karamar habaka y ayi ba da hanyoyi na zamani da makarantu manya da kuma asibitoci. Kuma babu ko daya daga cikin manyan biranenmu bakwai na Auyo da Kafin Hausa da Kirikasamma da Birniwa da Guri da Kaugama da Malam Madori da ba ya da kayatattun tituna da manyan asibitoci.

Muna da makarantar share fagen shiga jami’a da jami’a sukutun a cikin garin Kafin Hausa! Ko garin Elleman (’Yan Leman) da ke Karamar Hukumar Kaugama ba karamin birni ba ne idan za ka kwatanta shi da wasu garuruwan wani yankin.

Muna da hanyoyin mota na fita kunya da suka karade lungu da sakon yanki da kuma katafaren shrin aikin noma na Ma’aikatar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are da ya karade kananan hukomomi biyar daga cikin takwas na wannan yanki namu.

Dadin dadawa, ubanmu kuma shugabanmu Mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje Haruna CON shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jiharmu mai albarka. Wannan ba karamar karramawa ba ce da daukacin ‘yan uwanmu na Jigawa suka yi wa duk wani Bahadeje.

Ko a harkar siyasa ma da rubutun Malam Ilallah ya fi karkata, a cikin shekarun 23, wannan yanki ya fitar da Mataimakan Gwamna guda hudu da ministoci hudu, da shugaban majalisar jiha da manyan sakatarori a jiha da tarayya da manyan mukamai na nadi da kwarewar aiki a Gwamnatin Tarayya.

Na san Ahmed Ilallah da masu tunani irin nasa za su iya cewa ai duk wannan tagomashin bai kai ga kujerar Gwamna daya ba. Amsa ta gare su ita ce A’A. Domin a yau zancen da ake yi na cewa akwai wadanda suka fi kowa cancanta a takarar Gwamna a zaben badi, kusan uku daga cikinsu tsofaffi ne da Mataimakin Gwamna mai ci a yanzu, daya daga cikinsu tsohon Minista ne, biyu daga cikinsu nadaddune a Gwamnatin Tarayya.

To kun ga ‘yan uwana mai tafiya sama ya taka leda ai ya rage hanya. Domin kuwa akwai yankuna a Jigawa da ba su da irin wannan tagomashi da Allah da kuma ‘yan uwanmu al’ummar Jigawa suka yi mana. Na so a ce na yi wannan rubutu ban kama suna ba, ba don Malam Ilallah ya kama sunan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jagoran Jam’iyyar PDP a jihar wato Alhaji Dokta Sule Lamido (CON) ba.

’Yan magana na cewa gaskiya dai daya ce, daga kin ta sai bata. Hadeja ba ta samu wancan tagomashe ba sai da Allah Ya yi amafani da wannan bawan Allah wajen tabbatar da hakan. Alhaji Sule Lamido ne ya yi sanadiyyar nada marigayi Ambasada Daudu Suleiman daga kasar Hadeja a 1999 zuwa 2003 a matsayin Jakadan Najeriya a kasar Koriya ta Kudu. Kuma ya yi sanadiyyar zaman Ambasada Ahmed Abdulhamid Malam Madori a matsayin Minista a shekarar 2005 zuwa 2007.

Daga nan Ambasada Malam Madori ya zama wakilin Najeriya a kasar Turkiyya daga 2007 zuwa 2015. Ga wadanda ba su san harkar jakadanci ba, kasashe irin su Turkiyya da Koriya ta Kudu sai dan gata mai uwa a gindin murhu ke samu a cikin jakadunmu. Sannan Alhaji Sule Lamido ya sake sanadiyyar nada dan sarki, jikan Sarkin Hadeja, Alhaji Hassan Haruna a matsayin Minista daga 2007 zuwa 2009.

Alhaji Sule Lamido ya kuma daga likkafar matasan Jigawa domin haskaka su a kasa da duniya, a cikinmu ya zo ya dauko danmu mai hazaka wanda ba wai rasa irinsa aka yi a sauran yankunan Jigawa ba wato Dokta Nuruddeen Muhammad ya yi Minista lokacin yana da shekara 34 daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Da Allah ya sa Dokta Nuruddeen ya bar gwamnati kafin wa’adinta ya kare, ‘yar yankin nan Hajiya Hauwa Bello ’yar shekara 40 ya dauko ta maye gurbinsa.

A yau irinsu Dokta Nuruddeen su ne hasken da mu mutanen Hadeja muke ganin sun dau hanyar da wata rana za su iya kawo mana waccan kujerar da Ahmed Ilallah ya yi rubutu a kai. Kuma ya dace a sani lokacin da Hadeja take da wadancan mukamai a yankinsa na Dutse babu Minista ko Ambasada ko daya ka ga ke nan Dokta Lamido ya bai wa Hadeja kulawa.

Alhaji Sule Lamido ya gina mana Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a da Jami’ar Sule Lamido duk a garin Kafin Hausa. Ya gina mana Makarantar Koyar da Fasaha ta Bilyaminu Usman a Hadeja.

Ya gina mana hanya mai tsawon kusan kilomita 160 daga Kano zuwa Hadeja. Wannan hanya ba sai na yi bayanin amfaninta ga tattalin arzikin da zamantakewar wannan yanki ba. Ya yi mana hanya mai kyau da ta hada mu da Dutse.

Ya fito da katafaren dajin nan na Baturiya kan hanya tun daga Kwanar Arawa. Ya yi hanya daga Kwanar Auyo zuwa Kafin Hausa, ya yi tsohuwar hanya mai tarihi ta Hadeja zuwa Garun Gabas. Ya fara aikin hanyar Maigatari zuwa Diginsa har Birniwa. Ya gyara mana manyan makarantunmu masu tarihi.

Ya daga likkafar asibitocinmu zuwa manya, uwa-uba ya karrama tare da martabawa da mutunta masarautarmu mai daraja. Wadannan wasu ne daga cikin ni’imomin da Allah Ya yi amfani da Mai girma Alhaji Sule Lamido ya kawo mana a yankinmu.

Me ya kamata mu yi? Sai mu gode wa Allah sannan mu ci gaba da yi masa kyakkyawan zato da taya shi da addu’a da ci gaba da ba shi duk goyon bayan da zai bukata domin ci gaba da jagorancin al’umma cikin nasara da adalci.

Kujerar Gwamna allurar cikin ruwa ce mai rabo kan dauka. Abu ne da mutum daya ne kawai ka iya dauka a kowane lokaci. Rashinta a wannan yanki ba wai yana nufin don wani laifi da muka yi wa Sule Lamido ne ko Gwamna Badaru ba ne ballantana sauran mutanen Jigawa.

Lokaci ne na Allah, kuma duk lokacin da Allah Ya tabbatar da haka babu mai hanawa. Tabbas ne kamar yadda Malam Ilallah ya fada cewa mutanen Hadeja kan iya kin nasu su so wani, kuma wannan dalili ne ya sa gaba daya suka tattara kuri’unsu suka ba Alhaji Ali Sa’ad Birnin Kudu a 1992; suka tattara suka ba Alhaji Saminu Ibrahim Turaki daga Kazaure a 1999 da 2003; suka sake tattarawa suka ba Alhaji Sule Lamido a 2007 da 2011; suka kuma sake tattarawa suka ba Alhaji Badaru Abubakar Talamiz a 2015 da 2019.

Saboda haka ina da tabbacin cewa cikin ikon Allah haka su ma daukacin ‘yan uwanmu daga wadancan yankunan za su hadu wata rana su zabi mutumin wannan yankin a matsayin wanda zai jagoranci wannan jiha.

Mu mutanen Jigawa dukkanmu uwarmu daya ubanmu daya, harshenmu daya, addininmu daya, al’adarmu daya, komai namu daya. Sabani da zargi da rashin jituwa da jefa maganganu ana samunsu a zamantakewar da ta haura mutum biyu, ballantana dubbai da miliyoyi.

A karshe ina tunatar da Malam Ahmed Illalah cewa mu Hadejawa ba mu dauka cewa ‘yan uwanmu na sauran yankunan Jigawa suna zarginmu da aikata wani zunubi ba.

Zama ne idan ya yi zama ko hakori da harce hakuri suke yi, haka mata da miji, ballantana mutum da ‘yan uwansa na kusa har a zo zancen mutanen unguwa, zuwa gari da gunduma da yanki zuwa jiha baki daya. Jigawarmu dai ita ce abar alfaharinmu baki daya.

Adamu Mai Bada Shawara ga Dokta Sule Lamido kan watsa labarai ya rubuta daga garin Kafin Hausa, Jihar Jigawa.