Shugaba yana da muhimmanci fiye da yadda muke gani a Najeriya. Da shugaban ake gwada ci gaban kauye, gari, karamar hukuma, jiha da kasar, har duniyar ma a dunkule. A nan idan kuna da shugaban adali zai nuna kansa a kanku, tabbas za ku gani a kasa.
Harkar shugabanci ta sauya, dole sai an rungume mutane don ta yi armashi, sabanin yadda ake a baya, inda shugabanni kan nuna halin sarauta, saraki kuma kan wa talakawa bakin mulki. Ilimi da wayewar kai suka sa aka raina tsohon tsarin, musamman bayan ruhin dimokuradiyya ya dunkule duniya.
A yanzu dole sai shugaba ya bi mutane, ya kyautata kafin ya zama mai kwarjini, sarakuna suna musabaha, manyan mutane na halartar tarruruka a daidai kan lokaci, sabanin lokacin da fuskar shanu ma sai ta ba bawa kimma!
Wajen dawo da martabar kasa dole a samu shugabanni masu akida wadanda suka san mutunci. A haka bai kamata mutane su zabo shugabanni ko wakilai da zaran sun ga ana tallatar da su a sochiyal mediya watau feycbuk ko wazzaf, a san mutum a zahiri, a auna dabi’unsa.
A zabo shugaban daga cikin al’umma wanda aka sani, wanda yake kullawa da mutane kafin ya sami burin tsayawa takara, a lura ya alakarsa take da dalibai, matasa da talakawa, kafin ya fara zuba jari wajen samun mabiya!
Mai akida, wanda ya san mutuncin talaka, wanda yake kokarin kusantar ku, ba mai nisantarku ba, wanda zai auri ‘ya’yanku a cikin matansa hudu, don ya ceto marayu, ya tsare zaurawa, ya tallafawa iyalai da kabilu domin kara dankon zumunci.
Shugaban da zai nemo muku ayyukan yi, ta hanyar gayyatar kamfanonin kasashen ketare su bude rassa a garin ko mahaifarsa, ba daukar kudin ku ba da kaiwa kasashen ketare a aje masa asusu da sunan dansa na farko, kanensa ko matarsa don bada sawu.
Shugaban mai zuwa sallar asuba, wadanda muke gani a masallatai, ba wanda zai rufe kofa da karnuka! Wanda ya san kimar manoma da makiyaya, ba wanda bai damu da kowa ba sai mutanen banki, masu gidajen mai da ‘yan canji. Ya damu da damuwarmu.
Kar a zabi shugaban da yake da muradin neman kudi da mutane, ko ya bunkasa jarinsa, domin irin wadannan shugabannin sun fi yawa a yanzu, da zaran sun ci su gyara gonarsu, a wa gidaje kwaskwarima, a je kasashen da ba a je ba a baya, tsoho ya mayar da kansa matashi, a yi kara’i, a kulla sababbin huldodi.
A zabi shugaban da zai ceto jama’a, ya kai talaka tundun tsira, ba sarkin da ci gaban kansa ke gabansa, a duba ya yake da marayu, makwafta da makusanta. Wannan ita ce kyautatawa da sanin hakkin, ba wai raba kudi da neman suna, yana riyya, ana asarar dukiya a banza.
Irin shugaban da ba ya jure suka ko adawa, shugaban da yake kyamar wadanda yake mulka. Irin wadannan shugabannin hadari ne, ba su jin dadi sai idan talakawa na cikin duhu.
Tabbas idan akwai zaman lafiya ba wanda zai rika yawo da folis, ya kamata shugabaninmu su zama sadaukai, wadanda za su sadaukar da rayuwarsu don mu ji dadi, a tsaremu, su zama masu gadinmu, ba wadanda idan kuka matsa musu ba, su sa a dokeku, a daureku, su kai ku kotu, su lalata ‘ya’yanku.
Shugaban da ba ya cin hanci balle rashawa, wanda kan zauna cikin talakawa, ba wanda zai rika rigima yana neman mukamin da bai cancance shi ba, kawai don a ce shi ne shugaba, wai shi honorabul ko aikselensi.
Ka san akwai wanda ya fi ka cancanta, amma kana neman shugabanci, ta yaya zaka tafiyar da amanar da ke tatare da sarautar? A ba dan uwanka ko ka nuna wanda ka san ya fika cancanta, idan ba haka ba ka kawo gudummuwa wajen tauye al’umma.
Lokaci ya kusan zuwa da ‘yan siyasa za su sa birji a hanyoyinsu, wadanda ke kulle kofofinsu ga jama’a zasu bude, wayoyin da lambobin da suka bar aiki aka rufe za a samesu, fuskokin da suka bace a wajen daurin aure, gaisuwa ko sunan asuba za su rika bayana, kai kowane sati za su rika zuwa ko da zarar sun ji an yi rasuwa da su za a yi jana’iza!
Yanzu suka san darajar matasa, yanzu za su fito da kudi don su nuna ana tare, a nan ya za mu yi? Mu san masu son mu, ba wanda muke so ba, domin sau da yawa akan yi amfani da gajeren tunaninmu a mana babbar illa. Wai su masu iyayen gida, to wai haka ake neman aure? Daga an nemi izinin a wajen iyaye shi ke nan sai budurwa ta amince, wannan zamanin ake magana! ‘Yan yau.
Mu ma sai mun gyara, domin mutane nawa ne daga cikinku suke shirin gaya wa iyayen gidansu gaskiya a kasuwa ko a wajen aiki. Alaka ta amana ita ce taren da ake fahimtar yadda za a ci gaba, ba tare da an tade wani ba. Ko da ran mutum zai bace, amma an gaya masa gaskiya, ya fahimci haka shi ne so da kauna ta zahiri.
Da dama daga cikin mutane kan dauki wanda yake yaba musu a matsayin masoyi, bayan a zahiri wanda zai iya fada gaskiya don ka gyara shi ne masoyinka! Ko da ranka zai baci, domin za a gyara kuma a samu zaman lafiya. Ina fata Allah ya hada mu da abokai da shugabannin da za su tsaya tare da mu don mun fada musu gaskiya, gara ka samu aboki daya da zai gaya maka gaskiya a kan gari guda da zai ma munafunci wajen boye wa kuskuren da zai nakasaka a dogon zango.
Rashin cika alkawari bayan sauyi ko daukar nauyin marayu da zaurawa ya sa an gaza samun ci gaban a zo a gani da zarar uba ya rasu sai a bar gidan a bushe wani lokaci a yi kwanaki ba a dora tukunya kan wuta ba, ruwa ma sai an saya, haka a gwamnatance idan aka samu sauyi sai a yi watsi da duk ayyukan tsohuwar gwamnati duk muhimmancin su sai a barsu su rube! Ko da an kammala wadanda suke gab da kamalluwa sai sabuwar gwamnati ta nemi mallake aikin!
Matasa a bi a hankali domin ‘yan siyasarmu na da dabi’ar daukar matasa kamar ‘ya’yansu a rika wasa da dariya, su jaku jiki kamar da gaske, amma da zarar sun ci sai su jefa talakawa a kwandon shara! Ko musabaha ma an bari, balle kashewa ko zama tare, hange sai daga nesa! Dadin dadawa duk abin da suka samu a siyasance sai su yi wa ‘ya’yansu tanadi, ku kuma ku kuka! Talakawa sun zama ‘yan kai amarya.
A karshe a zabo shugaban da zai sa ‘yan kasa kishi, ya mayar da kasar abin alfahari, shugaban da zai dage wajen sulhu, ya zuba jari wajen sayo littattafai, ya gina laburari, ya bude gidajen jaridu, radiyo da tashoshin talabishin ba wanda zai wadata talakawa da mugan makamai ba ko kwayoyi don ya bugar da masoyansa!
Tabbas shugaba na gari shi ne wanda baya neman duniyar nan, shi ne wanda ya samu duniyar amma yake neman gyara lahirarsa. Shi ne shugaban da ya san mutuncin mutane. Ya Allah ka ba mu shugabanni masu karfin zuciya wadanda za su tsaya su daidaita, su yi adalci.
Buhari Daure [email protected] Modoji, Katsina.