✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Markade na kawo

Wani barawo ne wanda ya shahara a sata, wata rana sai ya afka wani gida da misalin karfe biyu na dare da nufin yin sata,…

Wani barawo ne wanda ya shahara a sata, wata rana sai ya afka wani gida da misalin karfe biyu na dare da nufin yin sata, ga duhu ko’ina. Da shigar sa,sai ya nufi can cikin gidan, bayan shigar sa, sai ya ga ko tafin hannun sa ba ya gani, sai ya fara laluben bangon gidan. Can sai ya ji makunnin wutar lantarki, sai gogan naka ya fara murna. Da kunnawarsa sai injin markade ya fara kara, sai masu gidan suka tashi a fusace suka ce: “Waye a nan?” Sai barawo ya gigice ya ce: “Markade na kawo!”
Daga Abdulbasir Abubakar Tingilin Malumfashi, 08099025522