Dan wasan gaban Ingila da Manchester United Marcus Rashford mai shekaru 25 ya yi hatsarin mota a Birtaniya.
Lamarin ya auku ne yayin da dan wasan ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan kungiyarsa ta Manchester United ta yi nasara kan Burnley a ranar Asabar.
- Mun kashe ’yan ta’adda 52 a Borno da Yobe — DHQ
- Diphtheria: Cutar mashaƙo ta yi ajalin mutum 10 a Jigawa
Bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna motarsa fara kirar Rolls Royce wadda darajarta ta kai fam dubu 700 a gefen titi bayan ta yi hatsarin.
Jaridun Ingila sun ruwaito cewa dan wasan bai ji rauni ba a hatsarin da ya rutsa da shi.
Rashford ya buga wasa na mintuna casa’in a filin wasa na Turf Moor inda kungiyarsa ta Manchester United ta ci Burnley 1-0, kwallon da Bruno Fernandes ya ci.
Wannan ne karo na farko da Manchester United ke cin wasa bayan kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni uku da ta yi a jere.