✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marcelo ya fara yunkurin barin Madrid a watan Janairu

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna cea dan kwallon baya Marcelo ya tattauna da shugaban kulob din Florentino…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna cea dan kwallon baya Marcelo ya tattauna da shugaban kulob din Florentino Perez a kan bukatar amince masa ya bar kulob din a watan Janairun badi.

Marcelo ya ce yana da sha’awar komawa kulob din Jubentus na Italiya ne don ya ci gaba da yin kwallo tare da Cristiano Ronaldo.

Marcelo, dan shekara 30 ya kwashe fiye da shekara 10 yana buga wa kulob din Madrid kwallo, yanzu hankalinsa ya fita daga kulob din inda yake neman canja sheka.

Rahotanni sun ce idan Marcelo ya canja sheka watakila hakan ya sa wadansu daga cikin ’yan kwallon kulob din irin su Luka Modric da Toni Kroos su fara tunanin barin kulob din.