✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maradona ya yi juyayin mutuwar Fidel Castro

Shahararren dan kwallon Ajentina Diego Maradona ya ce ya kadu matuka da ya samu labarin rasuwar shugaban kasar Cuba Fidel Castro.Castro wanda ya rasu yana…

Shahararren dan kwallon Ajentina Diego Maradona ya ce ya kadu matuka da ya samu labarin rasuwar shugaban kasar Cuba Fidel Castro.
Castro wanda ya rasu yana da shekara 90 a ranar Juma’ar da ta wuce bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya ana sa ran yin jana’izarsa ne a jibi Lahadi a kasar Cuba.
Maradona ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar Castro ne a kasar Kuroshiya a lokacin da ya isa don kallon wasan karshe na cin kofin Dabis Cup a tsakanin Ajantina da Kuroshiya.
Kamar yadda shahararren dan kwallon ya nuna, ya ce baya ga mutuwar mahaifansa, babu wata mutuwa da ta girziga shi kamar ta Fidel Castro, don shugaba ne da ya kasance yana ba shi shawarar da ta dace musamman wajen janyo hankalinsa don daina yin shaye-shayen kwayoyi.  “Ya rungume ni hannu bibbiyu a lokacin da wasu suke kyamata don haka ba zan taba mantawa da shi ba”, inji Maradona.
A jibi Lahadi ne ake sa ran za a yi jana’izar Castro inda ake sa ran halartar shugabanni daga sassan duniya.