Yabo da godiya da girmamawa da tsarkakewa sun tabbata ga Allah, Wanda Ya sanya dare da yini su kasance ma’aunan gane lokuta da kwanaki da shekaru da lissafe-lissafe.
Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta, Shugabanmu Annabi Muhammad wanda aka aiko shi don fitar da mutane daga duffan zalunci zuwa hasken adalci da imani da shiriya.
Bayan haka, a yau Talata ce cikin Yardar Allah muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 Bayan Hijira.
Hakika a cikin wannan juyawar lokaci akwai aya gare mu, domin wadansu da dama da muka ga wannan lokaci tare da su, a yau sun tafi sun bar mu. Allah Ya gafarta musu, mu kuma Ya sa mu cika da imani.
Baya ga kiyaye kwanakin watan Musulunci, zai yi kyau mu fahimci cewa yin aiki nagari shi ne babban abin da ake fata daga gare mu.
Ba mu zo duniya domin mu zauna ko mu tabbata ba, saboda haka mafi alherin guzurin da za mu yi shi ne takawa da aiki nagari.
Mun sha rubutawa cewa kidayar Kalandar Musulunci ta dogara ce da ganin jinjirin watan Muharram na kowane wata a kowace shekara ba a kan awoyi ko kwanaki bisa kintace ba.
Kuma kidayar watannin Musulunci ta samo asali ne tun daga ranar da Allah (SWT) Ya halicci sammai da kasa kamar yadda Alkur’ani ya nuna.
Amma tsarin kidaya ta dindindin da kuma kalanda don adana tarihi, ya samu ne a zamanin halifancin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (Allah Ya kara masa yarda), wanda ya dora mizanin kidayar a kan hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina bayan shawara da sahabbai.
Watannin Musulunci 12, yawan kwanakinsu ya dogara ne da ganin jinjinrin wata a ranar 29 ko 30 ga wata mai wucewa wanda wannan ya sa shekarar Musulunci ba ta wuce kwana 354.
Kuma kasancewar shekarar Musulunci ta ginu ne a kan Hijirar Annabi (SAW), wannan yana nuna cewa watan Muharram da shekarar hijirar an jingina su ne ga wani muhimmin al’amari da ya shafi addinin da daukakarsa da juyin juya-halin da ya kawo wa duniya baki daya tun daga wancan zamani zuwa tashin Kiyama.
Watan Muharram da hijira suna da muhimmin matsayi wajen sanin muhimman al’amuran addini.
Don haka sanin tarihinsu da abubuwan da suka faru a cikinsu tare da nazarin darussan da suke dauke da su suna da muhimmanci ga kowane Musulmi.
Allah Madaukaki Ya nuna cewa adadin watanni a wurinSa goma sha biyu ne, sai dai saboda duhun kafirci da shirka da al’adu da suke bayyana a kowace al’umma sai ya zamo kowace al’umma ta sanya watannin sun dace da al’adunta.
Misali a kasar Hausa sunayen watannin sun ginu ne a kan wasu abubuwa ko al’adu da suka shafi Hausawa, inda suke kiran Muharram da watan Shara wato watan wasan kaka da jika ko dan mace da dan namiji, ko su kira shi da watan Cika-Ciki.
Akwai watan Bawa na Juya-Bai da sauransu.
Haka su ma Larabawa sun jirkita sunayen watannin don su dace da al’adunsu, kafin Allah Ya sake mayar da al’umma a kan daidai saboda aiko Annabi (SAW).
Muharram da sauran watanni a tarihi:
Watan Muharram shi ne mabudin shekarar Musulunci. Muharram na daya daga cikin watanni hudu masu alfarma da hatta mushirikan Jahiliyya suke girmamawa.
Sauran watanni masu alfarma su ne Zul-Kida da Zul-Hajji da suke zuwa kafin Muharram.
Cikon na hudu shi ne Rajab da ke ware.
Larabawan Jahiliyya suna haramta wa kawunansu yaki a cikin wadannan watanni.
Watannin Musulunci 12:
1. Muharram 2. Safar 3. Rabi’ul Awwal 4. Rabi’us Sani 5. Jimada Ula 6. Jimada Akhir 7. Rajab 8. Sha’aban 9. Ramadan 10. Shawwal 11. Zul-Kida 12. Zul-Hajji
Dalilin kiransa da watan Muharram: Ya zo a cikin littafin Nihayatul Arab cewa dalilin da Larabawan Jahiliyya suka sanya wa watan farko na shekara sunan Muharram shi ne sun taba kai harin yaki aka yi galaba a kansu, don haka suka haramta wa kansu yaki a cikinsa, suka kira shi mai alfarma wanda ba a yaki a cikinsa.
Sai dai a zamanin Jahiliyya, jeranta watanni masu alfarma yana matukar wahalar da Larabawan saboda sabonsu ga yake-yake da kai hare-hare, don tara dabbobi wadanda su ne ginshikin tattalin arzikinsu ko don daukar fansa a kan wata kabila da ta taba su.
Don haka sai suka bullo da tsarin jinkirta watan Muharram ta yadda zai zamo babu wani wata mai alfarma face Zul-Kida da Zul-Hajji, sai su fara kidayar sabuwar shekara daga watan Safar.
Tarihi ya nuna cewa wani mutum daga kabilar Banu Malik bin Kinana da ake yi wa lakabi da Al-Kalamisiy shi ya shahara da wannan jinkirtawa.
Da ya rasu sai dansa Kali’u bin Huzaifa ya gaje shi. Kali’u ya riski Musulunci, amma Abu Tamama ne mutum na karshe da ya yada wannan al’ada ta jinkiri bayan Musulunci ya yi hani a kan haka.
Yadda Larabawa suke yin wannan jinkiri shi ne idan suka kammala aikin Hajji sai su taru a wurin mai bayyana jinkintawar, sai ya mike a cikinsu ya ce: “Ni na halatta Safar din farko kuma na jinkirta daya Safar din sai shekara mai zuwa.”
Bayan bayyanar Musulunci, sai watanni masu alfarma suka koma kamar yadda suke a farkon halitta, inda Allah Madaukaki Ya haramta jinkirtawar cikin fadinSa: “Abin sani kawai jinkintawar nan kari ne a cikin kafirci…”
Sannan Ma’aiki (SAW) a Hajjinsa na Ban-Kwana ya ce: “Ku saurara! Lallai zamani ya juya kamar yadda Allah Ya tsara shi a ranar da Ya halicci sammai da kasa.”
Wato yana nufin sunayen watanni sun koma kamar yadda suke a farkon halitta.
Kuma ga shi an haramta aiki da al’adar jinkirta wani wata don ya fada cikin wata shekara.
Wannan shi ne takaitaccen tarihin watannin Musulunci wadanda suka ginu a kan aiki da jinjirin wata da aka gani a samaniya maimakon lissafi da kakale-kakalen mutane.
Allah Ya datar da mu ga abin da ya fi zama daidai.