Sun hadu a Hunain wani kwari da ke tsakanin Makka da Da’ifa, Musulmi sun gabato suna cikin wannan kwari ya kasance wadanda ba su da makamai masu tafiya kasa su ne a gaba, kwatsam ba su yi aune ba, ashe mushirikai sun yi kwanton bauna suka fara yi musu ruwan kibau da masu. Ashe Banu Huwazin sun tanadi kwararrun maharba, duk wanda suka saita suka harba sai sun same shi, haka ya sa Musulmi suka rude suka hargitse su ma dabbobin da ake haye kansu suka gigice suka rika karo da juna mutane kuma suka ja da baya na bayansu ma suka koma suka gudu. Wannan ya faranta ran mushirikai.
Manzon Allah (SAW) yana nan tabbace a wurin da yake kan dabbarsa Ash-Shahba, tare da wadansu sahabbai cikinsu akwai: Abubakar da Umar da Abbas da Ali da Fadlu dan Abbas da Abu Sufyan dan HariS dan Abdulmudallib da Ayman da Usama dan Zaid (Allah Ya kara musu yarda). Manzon Allah (SAW) ya nufi wurin mushirikai ya juya dabbar sai Baffansa Abbas ya rike akalarta ta dama, Abu-Sufyan dan Haris dan Abdulmuddalib kuma ya rike ta hagu, suna rike da ita ce don kada ta yi saurin fadawa cikin makiya. A nan Manzon Allah (SAW) ya fada da karfi ya ce: “Lallai ni bawan Allah ne kuma lallai ni ManzonSa ne.” Ya sake cewa “Lallai ni Annabi ne ba karya, ni dan Abdulmuddalib ne.”
Manzon Allah (SAW) ya umarci Baffansa Abbas ya yi kira da madaukakiyar muryarsa, “Ya ku ma’abota Samurah (wadanda suka yi bai’a karkashin itaciya) ina kuke?” Nan da nan suka taho inda sautin yake suna ‘Labbaika! Labbaika!’
Ya ku mutanen Ansar! Sannan Khazraj, haka ya yi ta kiransu suna zuwa kamar yadda saniya take kiran ’ya’yanta, bayan sun taru Allah Ya saukar musu da natsuwa da saukar da wasu rundunoni wadanda ba sa gani. Daga nan Manzon Allah (SAW) ya umarce su da fuskantar mushirikai da yaki suna masu ikhlasi sai suka ci gaba da yaki sannan ya damki kasa da mai albarka ya watsa a fuskokin kafirai bayan ya yi addu’a ya ce: “Ya Allah ka cika alkawarin da ka yi mini!” Kasar ta shiga idanu da bakunan kafirai wanda hakan ya sa suka ja da baya suka rarrabu kuma suka gudu. Musulmi suka bi su suka kama su suka daure kuma suka tsare su. Wadansu kuma suka bi wadanda suka gudu, mushirikai kuma da yawa suka musulunta a wannan ranar saboda irin abin da suka gani na taimakon Allah a kan Musulmi. Da mushirikai suka gudu sun rabu kashi uku, mafi yawansu suka gudu Da’ifa, wadansu Nakhlah wadansu Autas.
Manzon Allah (SAW) ya tura Abu Amir Al’Ash’ari (Baffan Abu Musa Al’Ash’ari) da wadansu jama’a zuwa Autas, suka karya mushirikai amma dai Abu Amir ya yi shahada, sai Abu Musa ya maye gurbinsa suka dawo da ganima.
Musulmi suka bi wadanda suka gudu Nakhlah suka karya su kuma suka kashe Duraid dan Sammah a can.
Manzon Allah (SAW) ya ba da umarni a tattara ganimar gaba daya, an samu: Rakuma 24,000. Awaki fiye da dubu arba’in. Ukiya 4000 ta azurfa. Kamammu har da mata da yara 6000.
Darasi na Arba’in da Biyar
Yakin Ta’if
Bayan an gama da Autas, Musulmi sun wuce Ta’if sun tarar kafirai sun shige ganuwarsu sun kulle. Musulmi sun sauka kusa da su sai suka rika harbinsu da kibau har suka raunata wadansu Musulmi. Khalid yakan fita da safe ya kira su kan su fito a yi mubaraza (gaba-da-gaba) amma suka ki fitowa. Sai Musulmi suka rika jifarsu da majaujawa da wasu dabaru don su fito amma shiru. An samu wadansu gwaraza da suka yi nufin tumbuke kofar shiga garin sai dai haka ya faskara domin suna jefo jajayen karfuna da suka sha wuta a wurin. Da aka rasa samun wata natija ga shi an tsare su wajen kwana ashirin, sai Manzon Allah (SAW) ya shawarci sahabbai kan yadda za a yi. Sai Naufal dan Mu’awiyya Addaili ya ce su kamar dila ne idan aka tsaya kansa za a kama shi, idan kuma aka kyale shi ba zai cutar ba. Sahabbai ciki har da Umar (RA) sun ba da shawarar a dage mamayen Allah zai shirya faduwar maboyarsu, wadansu Musulmi suka nemi a yi musu addu’a sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Allah! Ka shiryar da Sakifa, Ka zo da su suna Musulmi.”
An kyale su, Annabi (SAW) da sahabbai suka juya zuwa Makka. Kabilar Huwazin suka musulunta suka zo suka samu Manzon Allah (SAW) a kusa da Ji’irana kafin ya kai Makka bayan kwana ashirin da yakin Hunain. Manzon Allah (SAW) ya ba su zabi cikin biyu ko a mayar musu da dukiyarsu ko a ba su kamammunsu? Sai suka zabi a ba su kamammun sai aka saki mutanensu 6000.
An raba ganima tsakanin mujahidai da wadanda ake kwadayin musuluntarsu sannan aka bai wa wadansu jagorori rakuma dari-dari, wadansu hamsin-hamsin haka dai. Manzon Allah (SAW) ya rabar da ganimar nan, ya bayar da ita irin kyauta ta wanda ba ya tsoron talauci. Kason mutum daya ko dai rakuma biyu ko kuma awaki arba’in. Da Manzon Allah (SAW) ya gama raba ganima sai ya yi Harama da Umara ya je ya yi sannan ya koma Madina kuma ya isa bai fi kwana uku ba watan Zul-Ki’ida ya kare.
Ladabtar da Banu Tamim
A shekara ta 9 Bayan Hijira ne aka kawo labari Madina cewa Banu Tamim suna kwadaitar da kabilu kan su hana jizya. Sai Manzon Allah (SAW) ya aika musu mahaya hamsin a karkashin jagorancin Uyainah dan Husunu Al-Fazari sai ya kai musu hari a cikin sahara ya kama maza goma sha daya daga cikinsu da mata ashirin da daya da yara talatin ya taho da su Madina. Wannan ya sa shugabanninsu suka zo Madina sai mai iya maganarsu ya yi magana, shi ma Sabit dan Kais daga bangaren Musulmi ya ba shi amsa. Sannan mawakinsu Zubrukan dan Badru ya rera waka, nan ma daga Musulmi Hassan dan Sabit mawakin Musulunci ya mayar da martani wanda ya sa suka yaba da ganin fifikon wadannan mutum biyu na Musulmi kuma suka musulunta. Daga nan Manzon Allah (SAW) ya mayar musu da kamammunsu ya kyautata musu.
A cikin watan Rabi’ul Awwal ne kuma ya aiki Aliyu dan Abu Dalib (RA) tare da mutum 150 suka je rusa gunkin Banu Tai’u wanda aka fi sani da Fulus, sun je suka kai farmakin suka samu ganima da kamammu. Akwai wata mata mai suna Sufana a cikinsu, sai Manzon Allah (SAW) ya sa aka sake ta ya ba ta rakumi ta hau ta tafi. Sai ta wuce Sham inda dan uwanta Addiyyu dan Hatim ya gudu, ta dalilin haka ya sa ya zo da kansa har Madina ya amshi Musulunci.
Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]