Dufail dan Amru shi ma yana cikin wadanda aka gargada game da Annabi (SAW) tun kafin ya gan shi, da ya isa Harami sai ya tottoshe kunnuwansa don kada ma ya ji abin da Annabi (SAW) yake cewa. Da ma shi mawaki ne sai aka yi sa’a Annabi yana Sallah a Ka’aba kawai sai Allah Ya nufe shi da jin wani yanki na karatun Annabi (SAW). Sai ya ce a ransa bari ma in saurare shi ai ni mawaki ne na san abu mai kyau da mummuna, idan mai kyau ne in karba idan mummuna ne in bar shi. Allah cikin ikonSa wannan bawan Allah ya fahimci gaskiya don haka da Annabi (SAW) ya koma gida ya bi shi ya karbi Musulunci. Ya nemi Annabi (SAW) ya yi masa addu’a Allah Ya sa masa wata alama da za ta sanya mutanensa su yarda da wannan addini, a nan Annabi (SAW) ya roki Allah kuma Ya amsa, Dufail yana komawa wajen mutanensa fuskarsa ta yi haske, ya kira su zuwa ga Musulunci mahaifinsa da matarsa da manyan wannan kabila suka musulunta, bayan Sulhun Hudaibiyya wannan Sahabi ya yi hijira zuwa Madina tare da iyalan gidaje 70 ko 80 na mutanensa.
Dimadul Azdiy: Shi ma mutumin Yamen ne yanayi wa masu shafar aljanu da shaidanu da tabin hankali (tawaida). Ya zo Makka sai ya ji wawaye suna cewa Muhammad mahaukaci ne, don haka sai ya je don ya yi masa tawaida yana zuwa kusa da shi sai ya ji Annabi (SAW) yana cewa:
“Innal hamdalillahi, nahmiduhu wa nasta’inuhu, wa man yahdihillahu fala mudillalahu, wa man yudililhu fala hadiya lahu. Ashhadu an la’ilaha illallahu wahdahu la sharikalahu, wa asshadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu.”
Sai kawai Dimad ya nanata sau uku ya ce, “Na ji bokaye da masu sihiri amma ban taba jin irin wannan ba,”shi ma nan take ya nemi Annabi (SAW) ya ba shi hannu ya yi masa mubayi’a.
A cikin shekara ta 11 da aike ne wadansu mutum shida daga Madina suka zo Makka aikin Hajji kuma suka karbi Musulunci mutanen su ne:
As’ad dan Zurara
Awfu dan Haris
Rafi’u dan Malik
Kutba dan Amir
Ukba dan Aamir
Da ma sun sha ji a wurin Yahudawa yayin da suke kai musu hari suna cewa yanzu ne za a aiko wani Annabi sai mun yake ku tare da shi, su a zatonsu cikin tsatsonsu na Yahudawa zai fito.
Wata rana Manzon Allah (SAW) ya wuce ta wurin wadannan mutane yake tambayarsu ku su su wane ne? Sai suka ce kabilar Khazraj daga Madina, ya ce iyayen gidan Yahudawa? Suka ce eh, ashe ba za ku zauna in yi magana da ku ba? Suka ce za su zauna, sai suka zauna tare da shi sai ya gaya musu hakikanin Musulunci ya karanta musu Kur’ani, nan da nan suka gaskata Annabi (SAW) suka ce a tsakaninsu wallahi shi ne wanda Yahudawa suke yi mana alkawari da zuwansa. Kada mu yarda su rigamu gare shi, a kan haka suka ce masa mun bar mutanenmu a cikin kiyayya da sharri a tsakaninsu, idan Allah Ya dora ka a kansu babu mutumin da zai samu daukakarka, in dai ka samu ka daidaita mu an samu fahimtar juna da zaman lafiya a tsakakaninmu a birnin Madina. Wadannan mutane sun yi masa alkawarin tsayuwa da kira ga addininsa da dawowa Hajjin shekara ta gaba.
Darasi na Ashirin da Hudu
Bai’ar Akaba ta Farko
Da shekara ta zagayo wadda ta yi daidai da shekara ta 12 da aiko Manzon Allah (SAW) mutanen Madina sun dawo amma wannan karon su 12 suka zo Makka, goma daga cikinsu ’yan kabilar Khazraj ne, biyu kuma daga kabilar Ausu. Wadannan kabilu guda biyu babu abin da ke tsakaninisu sai gaba da yaki a kowane lokaci, ga munafukan kabilun Yahudawa uku tare da su dama kuma fitina ta ishe su sun kosa da ita suna neman mafita ce a kanta, sai kuma ga Annabi (SAW) ya bayyana. Don haka wannan yana daga cikin manyan dalilan da suka sa suka shiga Musulunci, kuma suna ganin idan addinin ya daukaka su ma za a rika zuwa wajensu kamar yadda ake zuwa Ka’aba, sannan babban dalilinsu na yi imani da Manzo (SAW) shi ne tunda sun tabbatar da zuwansa a bakin Yahudawa kuma suna so su riga kaiwa gare shi kafin Yahudawan. Mutanen biyar daga cikin shida da suka zo shekarar da ta gabata, wanda bai zo ba shi ne Jabir dan Abdullah dan Ri’ab. Sauran su ne: Zakwan dan Abdulkais, Ubbada dan Samit, Yazid dan Sa’alaba. Al’abbas dan Ubbada dan Nadla dukansu ’yan kabilar Khazraj. Sai Abul Haisum dan As-Saihan da Uwaim dan Sa’ida daga kabilar Ausu.
Sun hadu da Manzon Allah (SAW) a Akaba ya sanar da su Musulunci kuma ya ce: “Ku zo ku yi mini mubaya’a a kan ba za ku hada Allah da komai ba, ba za ku yi sata ba, ba za ku yi zina ba, ba za ku kashe ’ya’yanku ba, ba za ku zo da kiren karya ba da hannayenku da kafafunku suka kirkira, ba za ku saba mini ba a wurin aikata kyakkyawan aiki. Wanda ya cika daga cikinku ladarsa na wurin Allah, wanda ya dace da wani abu na wannan to ukubarsa a duniya ita ce kaffararsa, wanda kuma ya dace da wani abu na wannan, Allah Ya suturta shi to lamarinsa na wurin Allah in ya so Ya yi masa ukuba kuma in Ya so Ya yi afuwa.” Sai suka yi masa mubaya’a a kan wadannan.
Bai’ar Akaba ta Biyu
Bayan shekara daya da yin bai’ar farko ga Annabi (SAW) a shekara ta 13 da aiko shi, mutanen Madina sun zo Makka aikin Hajji sai suka ce lallai ba za su bar Annabi (SAW) a Makka ba, don haka suka hadu da shi a cikin kwanukan Tashrik da dare a inda Jamratul Akaba take, shi ya sa ma ake kiran wannan bai’a da Bai’atul Akaba. Yawan mutanen su 73 ne, sittin da biyu daga kabilar Khazraj, goma sha daya kuma daga kabilar Ausu. Sai dai mata biyu ne kawai a cikinsu: Nusaiba ’yar Ka’ab daga Bani Najjar da Asma’u ’yar Amru daga Bani Salma.
Sun fita da daidai zuwa mutum bibbiyu ne don kada a gane wannan taro nasu da suka kulla na haduwa a asirce. Annabi (SAW) ya riske su a tare da shi akwai dan uwan mahaifinsa Abbas (RA) amma a lokacin bai riga ya karbi Musulunci ba, ya dai halarta ne don ya sa ido da samun aminci ga dan dan uwansa. Abbas (RA) shi ya fara magana ya nuna musu lallai fa Annabi (SAW) yana da izza a cikin mutanensa idan kun san ba za ku cika masa alkawarin da kuka yi ba, to tun yanzu ku kyale shi.
A wannan taron ganawa tsakanin Annabi (SAW) da wakilan mutanen Madina, an cimma wasu yarjejeniyoyi a tsakanin bangarorin biyu. Abubuwan da aka zartar a wannan taro su ne:
– Kada a yi tarayya da Allah wajen bauta
– Ka da a yi sata
– Ka da a yi zina
– Ban da kashe ’ya’ya mata
– Ban da jefa kalmomin kazafi a tsakanin juna
– Ban da saba wa Annabi (SAW) a dukan al’amura
– Yin biyayya ga umarnin Annabi (SAW) a cikin sauki da tsanani.
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]