Aminiya ta ruwaito cewa hafsoshin soja da dama sun rasa rayukansu a cikin watanni uku da suka gabata a cikin hadarurruka da jiragen sama na Sojan Najeriya suka yi.
A ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairun bana, wani jirgi mai suna Beechcraft KingAir B350i da ke kan hanyarsa ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja, ya yi hadari a kusa da titin da jirage ke sauka da tashi a Filin Jiragen Saman Abuja bayan ya ba da rahoton lalacewar injin.
Har wa yau, a ranar Laraba, 31 ga watan Maris din bana, wani jirgin yaki, wanda amfani da shi a yaki da ’yan ta’addan Boko Haram da kungiyar IS a Yammacin Afirka ya bace wa na’urar da ke hango jirage a sararin samaniya a Jihar Borno.
Na baya-bayan na shi ne wanda na Jirgin Sojan Saman Najeriya mai suna Beachcraft 350 da ya faru ranar Juma’a, 21 ga watan Mayun da muke ciki, wanda ke dauke da Babban Hafsan Sojan Kasan Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru.
Attahiru da wasu jami’an guda 10 da suke cikin jirgin sun mutu hadarin a kusa da Tashar Jiragen Saman Kasa da Kasa na Kaduna.
Sauran wadanda suka rasa rayukansu a ayarin na Babban Hafsan Sojan sune Birgediya Janal MI Abdulkadir da Birgediya Janal Olayinka, da Birgediya Janal Kuliya da Manjo LA Hayat da Manjo Hamza da Sajen Umar.
Matukan jirgin kuma sune Flt.-Lt.TO Asaniyi da Flt.-Lt. AA Olufade da Sajen Adesina da CM Oyedepo.
Aminiya ta kalato cewa, Manyan Hafsoshin Soji hudu ne suka rasa rayukansu a hadarin jiragen sama – uku yayin da suke ganiyar aiki, guda kuma bayan ya yi ritaya.
Sun hadar da; Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanar-Kanar Joseph Akahan (Mayun 1968) sai Babban Hafsan Sojan Sama, Laftanar Shittu Alao (15 ga watan Oktoban 1969, a Uzebba, kusa da birnin Benin) sai Hafsan Hafsoshi, Janar Andrew Owoye Azazi (15 ga watan Disamban 2012, a Bayelsa) sai Laftanar-Janar Attahiru a watan Mayun 2021.