✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Gobe barka da warhaka 9

Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Mairo da Dodo. Labarin ya kunshi yadda girman…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Mairo da Dodo. Labarin ya kunshi yadda girman kai ko jiji da kai ke kai mutum ga halaka. 

A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Mairo da Dodo

A wani kauye mai suna Kamfan an yi wata kyakkyawar budurwa mai suna Mairo. Fara ce, doguwa kuma kyakkyawa, tsabar kyawun idanunta idan ta kada su fari tas kamar madara suke komawa. Tana da dogon gashi mai yalki har baya. Domin ta san cewa ta fi kowace mace kyau a kauyen, sai ta rika ji da kai sosai.
Manema da dama suka rika zuwa wajenta amma ta ki aure ko daya a cikinsu. Ta ce ita sai mai kudi za ta aura. Wulakancin yau da na gobe daban.
Kakarta ta rika ba ta shawarar cewa ba a alfahari da kyau, domin wata rana za a rasa shi, domin tsufa ba ta barin kyawun ya dade, gara ta koyi dabi’u masu kyau, domin tsufa ba ta da tasiri a kan dabi’u masu kyawu.
Rannan sai labarin ya isa kunnen wani dodo. daga nan ya yi shigar mai kudi. Daga ganin sa ta amince da shi suka yi aure. Ya tafi da ita kasarsu ta dodonni. Haka ya rika gallaza mata. Da kyar wani Bafulatani ya taimaka mata ta dawo gida.
Manyan Gobe a zama yaran kirki, kuma kada a rika ji da kai domin yin hakan.