✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Gobe barka da warhaka 08

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon kawunku Naseeru Taneemu ne ya kawo muku labarin Tanko da Gambo. Labarin ya kunshi yadda ya…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon kawunku Naseeru Taneemu ne ya kawo muku labarin Tanko da Gambo. Labarin ya kunshi yadda ya kamata a rika kyautata wa makiyi.
A sha karatu lafiya
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Tanko da Gambo

A wani gari mai suna Durmi akwai wani mutum mai suna Tanko. Yana da farin jini saboda yana kwatanta gaskiya da rikon amana a duk sha’aninsa. Wannan ya sa kowa yake kaunarsa, amma ban da makwabcinsa Gambo.
Ba komai ba ne ya haddasa kiyayyar Tanko a zuciyar Gambo ba face ganin yadda Tanko yake samun ci gaba a sana’arsu ta sayar da kayan miya. Tanko yana da araha, kayansa suna da inganci, shi kuma  Gambo saboda son kai, tsada da rashin ingancin kayan miyarsa ya sa mutane suke tsallake shi zuwa rumfar Tanko. Wannan abin yana matukar damun Gambo, kullum yana tunanin hanyar da zai bi ya nakasa kasuwancin Tanko. Duk wannan makarkashiyar da Gambo yake yi Tanko ba shi da masaniya.
A kwana a tashi rannan aka kawo wa Tanko kayan miya cikin mota har kofar gidansa. Da yake ba mutanen da za su taya shi saukewa, sai ya nemi taimakon Gambo ya zo su sauke. Shi ko Gambo sai dama ta samu, yau ga yadda zai huce hushinsa.
Bayan sun gama sauke kayan, sai Tanko ya yi godiya sosai, sannan ya dauko kwandon tumatir ya ba shi, ya karba ya shige gidansa zuciyarsa cike da farin ciki.
Da asubar fari matar Tanko ta sanar da shi an yi musu sata, daga nan suka nufi dakin da suka ajiye kayan miya a jiya. Bayan sun ga ta wurin da aka shiga ne, sai Tanko ya fara zargin Gambo.
Suna tsaye cikin jimani sai suka ji ana salati a gidan Gambo, cikin hanzari suka nufi gidan inda suka tarar dan Gambo cikin mayuwacin hali da kyar yake numfashi.
Tanko ya tambayi matar Gambo ina yake, inda ita kuma ta ce rabon da ta gan shi tun jiya da daddare. Ba tare da bata lokaci ba Tanko ya kai yaron asibiti.
Da yammancin ranar ne Gambo ya dawo gida inda matarsa Umaima ta ba shi labarin abin da ya faru. Jin haka, sai jikinsa ya yi la’asar, hawaye suka zubo daga idanunsa. Yanzu a ce mutumin da ya tsana, kuma yake cutarwa shi ne yake taimakonsa?  Ba tare da bata lokaci ba Gambo ya nufi gidan Tanko inda ya nemi gafarar sa. Kasancewar Tanko mutum ne mai saurin yafiya, sai ya yafe masa. Tun daga wannan rana Gambo ya dawo mutumin kirki, arzikinsa ya fara bunkasa.