✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Gobe barka da warhaka 02

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon na kawo muku labarin Zuma da Biri. Labarin na kunshe da…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon na kawo muku labarin Zuma da Biri. Labarin na kunshe da darasin idan ka aikata kuskure, to ganganci ne ka sake aikata wannan kuskuren. Ya kamata idan ka aikata wani kuskure sai hakan ya zama maka wani darasi da zai sanya ka fahimci illar da ke tattare wajen aikata wannan kuskuren.

Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don ku fa’idantu da darussan labarin.
A sha karatu lafiya.
Naku Bashir Musa Liman

Labarin Zuma da Biri

A wani lokacin da ya wuce akwai wani biri mai kwadayi, wata rana yana cikin tafiya sai ya hango gidan zuma, yawun bakinsa ya tsinke musamman ma da ya tuna irin zakin da zuma ke da shi, cikin sauri ya nufi wurin, bayan ya raya a ransa kamar ya yi tsalle ya fada gidan zumar nan don ya kwashi dadin zumar, amma sai ya tsaya cik bayan ya hango zugar zumar suna ba da wani sauti. Nan take wani abu ya darsu a ransa. Ya tuna a makon jiya ne ya yi yunkurin lasar zuma amma a karshe zugar zuma suka rika harbinsa, inda da kyar ya kai labari. Ya tuna zafin da harbin zuma yake da shi, nan da nan bakin ciki ya mamaye shi.
Yana tsaye sai wata zuma ta zo wucewa, hakan ya sanya ya tambaye ta: “Da yaya kuke yin wannan sakar zuma mai dadin gaske, sannan kuke harbi mai tsananin radadi?”
Bayan ta je ta dawo sai ta ce masa: “Tabbas ruwanmu akwai dadi, amma duk wanda ya yi yunkurin diba to zai gamu da fushin harbinmu mai tsananin radadi.” Daga nan ba ta ce masa komai ba, ta wuce abin ta.
Bayan ya ja dogon numfashi sai ya ce: “Idan na ce zan sha zumar nan na san abin da zai biyo baya, don haka bari in yi wa kaina kiyamul-laili.”
Daga nan ya ci gaba da tafiya yana kallon gidan zumar.