A ranar Talata ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da babban kamfanin sarrafa takin zamani a Jihar Legas, wanda attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya gina.
Da wannan ne Aminiya ta yi waiwaye kan jerin ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar a birnin na Ikko tun daga farkon mulkinsa a shekarar 2015 zuwa 2022.
- Dan sanda ya mayar da N600,000 da aka tura masa bisa kuskure
- Jamilu Gwamna ya nemi afuwar PDP a bainar jama’a
Manyan ayyukan da Shugaba Buharin ya kaddamar sun hadar da ayyukan da gwamnatin tarayya ta aiwatar da kuma wadanda gwamnatin jihar Legas din ta samar wandan da suka hadar da sabbin gine-gine, hanyoyi da kuma kamfaoni a yunkurinsu na ci gaba da farfado da tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Manyan ayyukan sun hadar da:
- Kaddamar da masana’antar takin zamani ta Dangote da sauran ayyuka a Legas a ranar Talata, 22 ga watan Maris, 2022.
- Kaddamar da sabbin gine-ginen da aka kammala a filin jirgin saman Legas wanda suka hadar da babban dakin saukar fasinja da zai iya saukar fasinjoji miliyan 15 a duk shekara, sabon otal , dogon benen wurin ajiye mota da wurin shakatawar fasinjoji a ranar Talata, 22 ga watan Maris, 2022.
- Kaddamar da aikin da gwamnatinsa ta kammala na Tashar Jiragen Kasa ta Mobolaji Johnson da ke Ebutte Metta a Jihar Legas a ranar Alhamis 10 ga watan Yunin 2021.
- Kaddamar da dakin gudanar da wasanni maicin mutun dari hudu a yankin Oregun dake jihar Lagos da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta Lagos ta gudanar a ranar Laraba, 24 ga Afrilun 2o19.
- Kaddamar da sabbin jiragen ruwa na yaki a tashar jiragen ruwa da ke tsibirin Victoria Island a birnin Legas a ranar 9 ga Disamban 2021.
Bayanai sun ce kamfanin sarrafa takin zamani wanda Buharin ya kaddamar na nan a yankin Ibeju Lekki a Lagos, wanda aka bayyana ya lakume dala biliyan 2.5.
Kamfanin zai samar da ton miliyan uku na takin zamani duk shekara.
Kamfanin takin na Dangote zai taimaka wa Najeriya rage dogaro da takin da ake shigo da shi daga kasashen waje.
Haka kuma kamfanin zai taimaka wa kasashen Afirka dogaro da kansu wajen samar da abinci da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje.
Kaddamar da kamfanin na zuwa a daidai lokacin da farashin taki ya tashi sakamakon yakin Rasha a Ukraine, inda Rasha ce wadda ta fi samar da takin zamani a duniya.