Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Madalla da Allah, Wanda Ya sanya laushin zukata a cikin yawaita yi maSa da’a, kuma muna neman tsarinSa daga kutsawa cikin saba maSa, wanda ke sa kekasar zuciya.Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun kwana a daidai inda muka fara bayani a kan sinadari na shida, a cikin wannan mukala, to bari mu somo daga farkonsa. In mai karatu ya tuna mun jero sinadarai kamar haka: Sinadarin zikiri da na kiyaye gabobi daga sabo da na yawaita karanta tafsirin Alkur’ani Mai girma da na halartar darussan malamai da kuma na karanta littattafan malamai masu aiki da iliminsu wajen tsoron Allah. To, ga karashensu:
(6) Ziyartar Makabarta:
Yana daga cikin sinadaran da ke sassauta kekasar zuciya, mutum ya rika ziyartar makabarta yana ganin yadda kaburburan jama’a suke jere a ciki, tsoho da sabo; na yara da na manya daban-daban; ga su nan kwankwance babu wanda yake motsi. Ba ma zai yiwu su motsa din ba, domin sun rigaya sun bar wannan duniyar mai karewa. Ganin wannan zai sa mutum, in Allah Ya so, komai bushewar zuciyarsa, ya dan karyo, ya komo hayyacinsa, ya tuna cewa wata rana fa shi ma zai kasance cikin wadannan jerin.
Ziyarar makabarta ko kaburbura, wani aiki ne daga cikin ayyukan shiriyar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma ita ce mafi yalwar hujja da bayanin cewa wannan rayuwa takaitacciya ce, ba yadda za a yi ta wuce iyakar da aka tsaida mata, duk runtsi!
Idan an gane haka kuma, za a iya hakkakewa cewa tunda kowane abu na rayuwa takaitacce ne, to ba za a rudu da yawaitar buri, wanda yake abin zargi ba. Babu shakka kowane mutumin kirki yana da burin akalla ya samu wani abin da ya ajiye ko ya gabatar don ganin, ko bayan rayuwarsa wannan ta duniya, yana da wani abin da zai rika samun ladarsa, wato sadakatul jariya – sadaka mai gudana.
Dangane da tausasa zuciya kuwa wajen wannan ziyara ta makabarta, sau nawa ne? Wato manufa, da yawa, mutanen kirki salihan bayi sukan zubar da hawaye masu yawa a yayin da suka ziyarci makabarta, saboda tsoronsu ga Allah, suna tuna masaukinsu yadda zai kasance, in sun mutu!
Ita wannan ziyara ta kaburbura, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “…Lallai ita (ziyarar kabari) tana tunatar da ku Lahira…” Imamu Tirmiziy da Ibnu Majah ne suka fitar da Hadisin.
dauraya
Wadannan sinadarai da suka gabata a takaice, suna daga cikin magungunan kekasar zuciya, su sanya ta yi laushi ta yadda za ta gane matsayinta na baiwar Allah, mai tausayi da jinkai da tausasawa a cikin al’amuranta.
In mai karatu ya waiga baya, zai ga cewa farkon abin da aka yi nuni gare shi shi ne na yawaitawa cikin tunawa da kuma ambaton Allah, Subahanahu Wa Ta’ala, ta yadda a karkashin haka komai bushewar zuciya, in dai aka dimanci wadannan zikirori, to babu shakka za ta komo hayyacinta, ta natsu kuma ta yi laushi. Da wannan manufa ne ma Malam (Dokta Abdulmuhsin bin Muhammad Alkasim – cikin littafin nasa Khuduwatun Ilas Sa’adah) ya kawo:
Wasu nau’uka daga zikiri
1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Mafi soyuwar kalami ga Allah (shi ne a rika fadin) Subhanallah – wato Tsarki ya tabbata ga Allah; Walhamdulillah – Godiya ta tabbata ga Allah; Wa la’ilaha illallah – Babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah; Wallahu akbar – Allah ne Mafi girma.” Imam Muslim ne ya ruwaito shi.
2. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wala haula wala kuwwata illa billah – Babu wata dabara, babu wani karfi, sai tare da Allah kadai, – wannan wata taska ce daga cikin taskokin Aljanna.” Muttafakun alaihi – Buhari da Muslim (da sauran marubuta Hadisi) suka fitar da shi.
3. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wanda ya ce, ‘Subhanallahi wa bi hamdih’ – Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah – an yi masa dashen wani irin dabino a cikin Aljanna.” Imamu Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
4. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Kalmomi biyu masu saukin fadi a harshe, masu nauyi a kan mizani (ma’auni), ababen soyuwa wajen Mai rahama, su ne, ‘Subhanallahi Wa bihamdihi, Subhanallahil azim.’ – Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah, Tsarki da daukakar girmamawa sun tabbata ga Allah.” Muttafakun alaihi – Buhari da Muslim (da sauran marubuta Hadisi) suka fitar da shi.
5. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Walhamdulillahi – Godiya ta tabbata ga Allah, tana cika mizani; Subhanallahi walhamdulillah – Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah, masu cika mizani ko kuma suna cika abin da ke tsakanin sammai da kasa.” Imamu Muslim ne ya ruwaito shi.
6. An samo daga Sa’ad bin Abu Wakkaas (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Mun kasance a wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce, “Shin dayanku zai iya aikata aikin kwarai (hasanatun) dubu a kowace rana?” Sai wani ya yi tambaya, ‘Yaya za a yi mutum ya iya aikata aikin kwarai dubu a rana?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ya yi tasbihi (Subhanallah) dari, sai a rubuta masa (matsayin) aikin kwarai dubu ko kuma a kankare masa kura-kurai dubu.” Muslim ne ya ruwaito shi.
A karshe, Allah Yana cewa, “…Bone ya tabbata ga makekasa zukantansu daga ambaton Allah. Wadancan suna cikin wata bata bayyananna. Allah Ya sassaukar da mafi kyaun labari, Littafi (Alkur’ani) mai kama da juna (dangane da ayoyinsa), wanda ake kokkoma karatunsa (dare da rana, ba a gajiya, kodayaushe kullum kamar dai shi sabo ne), fatun wadanda ke tsoron Ubangijinsu, suna takura (suna taka-tsantsan, suna kaffa-kaffa) saboda shi (saboda karanta shi ko kuma da jin ana karanta shi)…” Suratu Zumar, aya ta 22-23.
Wato zukatansu suna laushi, suna komawa ga Ubangijinsu, ba su kekashewa (su bushe, su taurare) saboda mayar da hankalinsu da suke yi wajen ambaton Allah da neman kusanta zuwa gare Shi.
Alhamdulillahi! wannan shi ne dan abin da muke iya samu dagane da sinadaran da ke tausasa kekasar zuciya da fatan Allah Ya sa mu dace da alheran da ke ciki.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!