Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne, kamar yadda muka fada a makon da ya gabata, kan ladubban yin addu’a, kuma za mu takaita ne a kan abin da yake cikin littafin Al’azkaar na Imam Abu Zakariyya Yahya bn Sharf Annawawiy, sai dai inda bukatar wani abu ta taso. Muna fata Allah Ya ba mu dacewa, amin. Malam ya ce:
Babi A Cikin Ladubban Addu’a
Ka sani (ya kai mai karatu) cewa manufa zababba, wadda fukaha’u (malaman furu’a) da masu hadisi da masu yawa na malamai a cikin salafu (magabata) da khalafu (wadanda suka maye gurabun magabata), suka tafi a kan ta, ita ce cewa yin addu’a abin so ne.
Allah Ta’aala Ya ce a cikin Sura ta 40 (Ghaafir), aya ta 60: “Kuma Ubangijinku Ya ce, ‘Ku kira (roke) Ni in karba muku…” Haka nan Allah Ta’aala Ya ce, “Ku kirayi Ubangijinku da kankan da kai da kuma a boye….” Surar A’raaf, aya ta 55. Ayoyi da suka danganci wannan al’amari na addu’a masu yawa ne kuma sun shahara.
Su kuwa hadisai ingantattu game da addu’a, ya gabata a inda aka yi magana kan Kitabu Jami’ud Da’waat, daga shafi na 387 zuwa nan shafi na 395, lamarinsu ya kai matuka ta gamsarwa, saboda haka ba sai mun sake ambata su a nan ba – Da Allah muke neman muwafaka!
Mun ruwaito a cikin ‘Risalat Al’imamu Abiy Alkasim Alkushairiy’, Allah Ya jikan shi, inda ya ce: “Mutane sun yi sabani cikin cewa shin abin da ya fi shi ne a yi addu’a ko kuma a yi shiru, a yarda da hukuncin Allah?: (1) Daga cikinsu akwai wadanda suka ce, ai ita addu’a, ibada ce, kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna (wato wanda Imam Ahmad da Haakim suka ruwaito, kuma Shaikh Nasiruddinil Albaniy ya inganta shi a cikin littafin Sahihul Jami’u, hadisi na 3,407. Haka nan wasu daga cikin As’habus Sunan, wato Attirmdhi da An-Nasa’i da Ibnu Maajah; sai kuma Ibnu Abiy Haatim da Ibnu Jarir, sun fitar da shi kuma Imam Attirmidhi ya ba shi darajar “Hasan Sahih”), kuma saboda shi yin addu’a bayyanar da gazawa ce ga Allah Ta’aala, saboda haka ana da bukata daga gare Shi.
(2) Amma wasu suka ce yin shiru da kamewa da komawa karkashin magudanar hukunci (abin da Allah Ya kaddara) shi ya fi cika, wato da yarda da abin da ya riga ya gabata na kaddara, shi ne ya fi kamata a koma masa.
(3) Wasu sashe na jama’a suka ce, shi ma’abucin yin addu’a, sai ya kasance yana yin ta da harshensa (wato yana furuci da addu’ar), zuciyarsa kuma tana yarda (tana amincewa) da abin da yake aukuwa daga al’amurran guda biyu (kaddarar da kuma nuna gazawa ga Allah da bukatuwa gare Shi).”
Malam Alkushairiy ya ci gaba da cewa, “Abin da ya fi a ce shi ne, lokuta mabambanta ne. Wani lokaci a yi addu’ar shi ya fi a kan a yi shiru, kuma haka shi ne ladabi; kuma a wani lokaci a yi shirun shi ya fi a kan a yi addu’ar, hakan kuma shi ma shi ne ladabi; duka ana gane haka dai tsakanin al’amuran guda biyu, a kan lokacin; idan (mutum) ya ji a zuciyarsa cewa yana bukatar ya yi addu’a, to yin addu’ar shi ya fi; idan kuma ya sami isharar ya yi shiru, to shi ke nan yin shirun ya fi cika.”
Ya ce, “Abin da ya fi inganta shi ne a ce: Abin da yake cikinsa akwai nasibi (abin da za a samu) ga musulmi ko kuma ga Allah Tsarkakken Sarki akwai hakki a ciki, to yin addu’a shi ya fi domin kasancewarta ibada; idan kuma akwai wani rabo a kanta game da mutum, to yin shiru shi ya fi cika.”
Ya ce, “Yana daga sharuddan (samun karbuwar) addu’a, ya kasance abincin mutum halal ne.” Dalili a kan haka shi ne abin da Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa, hadisi na 1,015, cikin zakkah, babin karbarta daga cikin abin da aka samu mai tsarki (wato na halal). An samo daga Abiy Hurairata, Allah Ya yarda da shi, ya ce, Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Ya ku mutane, lallai Allah Mai tsarki ne, ba Ya karba, sai abu mai tsarki. Kuma lallai Allah Ya umurci muminai da abin da Ya umurci mazanni, inda Ya ce, ‘Ya ku Manzanni! Ku ci daga abubuwa masu dadi, kuma ku aikata aikin kwarai. Lallai Ni, ga abin da kuke aikatawa, Masani ne.” Suratul Mu’minun, aya ta 51. [A Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma, Shaikh Abubakar Mahmud Gumi ya ce, “Allah Ya umurci ManzanninSa da cin halal, sa’annan kuma su aikata aikin kwarai. Haka kuma Ya umurci muminai. Saboda haka karbar aiki na kwarai an tsayar da shi ne a kan cin halal.”].
“Kuma Ya ce, “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga dadadan abubuwan da Muka azurta ku (da su), kuma ku yi godiya ga Allah, in har kun kasance a gare Shi kadai kuke yin bauta.” Suratul Bakarah, aya ta 172. Sannan (Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ba da labarin wani mutum da yake cikin doguwar tafiya, kansa a hargitse (buzu-buzu), jikinsa da kura, yana mika hannayensa sama (yana cewa), ya Ubangiji, ya Ubangiji (yana rokon Allah bukatunsa) alhali abincinsa na haram ne, abin shansa na haram ne, tufafinsa na haram ne, an ciyar da shi haramun, ta kaka za a amsa masa?” [A Tarjama Da Sharhin Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma, Shaikh Ja’afar Mahmud Adam, ya ce, “Wannan aya da hadisi, suna nuna kwakkwarar alakar da take tsakanin cin halal da ingantuwar ayyukan ibadar bawa da amsa addu’arsa. Cin halal sababi ne na ingancin aiki da karbuwar aikin bawa ko addu’arsa, saboda haka wajibi ne ga musulmi ya yi kokarin nesantar haram game da abincinsa ko abin shansa ko tufafinsa ko abin hawansa ko muhallinsa da sauransu.”].
Yahya bn Mu’az Arraaziy, Allah Ya jikan shi, yana ce wa (Allah), “Yaya za a yi in rokeKa, alhali ni mai sabo ne? Kuma yaya za a yi ba zan rokeKa ba, alhali Kai, Mai karimci (Kariimi) ne?”
Nan za mu dakata, sai mako na gaba, in Allah Ya nufe mu da kaiwa za mu ci gaba. Wassalamu alaikum warahmatullaah!
Manuniya kan ladubban yin addu’a
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da…