Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta koka kan yadda wasu manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke haddasa taɓarɓarewar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi a Najeriya.
ACF ta kuma yi gargaɗin cewa Najeriya na iya fuskantar ruɗanin zamantakewa, musamman a yankin Arewa idan ba a yi wani abu ba don magance taɓarɓarewar tattalin arziki.
Ƙungiyar ta ACF ta bayyana hakan ne bayan yin taron majalisar zartarwa ta ƙasa da ta gudanar a Kaduna ranar Talata.
Ta ce ta lura cewa ana a ci gaba da rayuwa cikin wahala da ƙalubale, inda kullum talakawan Najeriya ke fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi, da saurin taɓarɓarewar rayuwa tare da tashe-tashen hankula, aikata ta’addanci da kuma barazanar ‘yan bindiga.
- ’Yan kwadago sun yi watsi da tayin mafi karancin albashin N54,000
- Yakin aiki: Ba gudu ba ja da baya —Kungiyoyin Kwadago
A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar kuma ya sanya wa hannu, ya koka da yadda matsalolin suka ci gaba da taɓarɓarewa a wasu wurare musamman a Arewa.
Ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a kan cire tallafin man fetur, da kuma haraji da gwamnatin tarayya ta yi, yana mai cewa waɗannan manufofin ne ke haifar da raguwar walwalar yanayin rayuwar ’yan ƙasa.