✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma sun samu sauki saboda injinan casar da muke kerawa – Abubakar Mai Walda

Alhaji Abubakar Garba Maiwalda, dattijo ne mai shekara 99 da ya shahara wajen  hada injinan casar kayan amfanin gona da suka hada da shinkafa da…

Alhaji Abubakar Garba Maiwalda, dattijo ne mai shekara 99 da ya shahara wajen  hada injinan casar kayan amfanin gona da suka hada da shinkafa da masara da gero da dawa da waken soya da farin wake da sauransu. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda yake hada injinan, inda ya ce manoma sun samu sauki saboda injinan da suke kerawa:

 

A yanzu kana da shekara nawa a duniya?

A yanzu ina da shekara 99. Kuma ina da ’ya’ya 28 maza 14, mata 14  kuma duk sunan nan a raye.

A wanne lokaci ka fara wannan sana’a?

Na fara wannan sana’a ce tun lokacin da na yi aiki a wani kamfanin na Turawa na hakar kuza a garin Bukur da ke kusa da Jos, fadar Jihar Filato.

A lokacin da na yi aiki da kamfanin, mu ne muke yin waldar duk wasu karafuna da suka karye  ko mu hada wani karfe da aka nema aka rasa. Na yi shekara 19 ina aiki da Turawa a kamfanin. Na bar kamfanin, na yi ritaya a 1984.

Daga nan na dawo garin Saminaka da ke Jihar Kaduna na bude wajen aikin sana’ar walda a tashar mota ta garin. Na yi shekara 17 a tashar ta Saminaka. Daga baya da na ga wuri ya fara cika, sai na taso na dawo garin Unguwar Bawa,  bayan da na samu babban fili  na bude wannan wuri.

To, kamar wadanne irin injina kake yi a nan?

Ina yin injinan casar kayan amfanin gona da suka hada da wake da waken soya da  masara da gero da dawa da shinkafa da dukan injinan casar kayan amfanin gona, muna yin su a nan.

Kuma muna yin injinan nika karan masara da totuwar masara wato kodagon masara, mu nika shi mu mayar da shi abincin dabbobi.

Yaya ka ga yanayin yadda manoma suka karbi injinan da casar da kuke yi?

Manoma sun karbi injinan da muke yi hannu babbiyu. Babu wani manomi da ya zo nan ya sayi injin casa da bai zo daga baya ya yi mana godiya ba. Domin injinan casarmu a rana manomi zai iya casa masara ko shinkafa ko gero ko wake buhu 200 zuwa buhu 300.

Wace gudunmawa kake ganin kun ba manoman wannan yanki da kasa baki daya?

A gaskiya injinan casar kayan amfanin gonar da muke yi a nan muna sayar da su da sauki domin kudaden da muke sayar wa manoma injinan, ba haka ya kamata mu sayar ba. Amma saboda mu taimaka wa manoman muke sayar masu da sauki. Misali kamar injin da ya kamata a sayar a Naira dubu 300 sai mu sayar musu a kan Naira dubu 200. Kuma muna ba manomi lambar waya, idan wani abu ya samu  inji sai ya kira mu, mu zo mu gyara masa ba tare da ya biya komai ba. Kafin manomi ya kara biyan wani abu a wannan inji da ya saya, sai ya yi sama da shekara daya yana amfani da shi.

Don haka sakamakon injinan da muke yi a nan manoma sun samu sauki sosai. Saboda kayan amfanin gonar da a da sai dai a buga da sanda yanzu manoma sun samu sauki, saboda injinan da muke kerawa. Ka ga a nan ya nuna cewa mun bai wa manoman kasar nan babbar gudunmawa.

Daga lokacin da ka bude wannan wuri zuwa yanzu ka yaye yara kamar nawa?

A gaskiya na yaye yara da dama. Domin yaran da na yaye wadansu sun je sun bude a wasu garuruwa kamar 6. Kuma na yaye ’ya’yana na cikina su 4.  Yanzu kuma na sake diban sababbin yara 4,da zan koya masu wannan aiki.

Ko akwai taimakon da kake bukatar gwamnati ta yi muku, ganin irin gudunmawar da kuke bai wa  manoma?

Muna bukatar kayayyakin aiki da ba mu da su. Domin da za mu samu wasu kayayyakin aiki za mu yi abubuwan da za su wuce kayayyakin da muke yi. Ka ga yanzu muna son mu rika yin injin casar da zai rika kai kansa gona, ba tare da sai an ja shi ba. Amma ba mu da kayayyakin aiki da karfin da za mu yi hakan, don haka akwai bukatar gwamnati ta tallafa mana.

In da gwamnati za ta tallafa mana, ba sai an rika fita waje ana shigo da injinan casar kayan amfanin gona ba.

Ka ga misali kamar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar a bara ya turo wani jami’insa nan wajen, na yi masa injinan casa guda 12. Aka zo da tirela 2 aka kwashe su aka tafi da su Yola.

Don haka idan gwamnati za ta tallafa mana da kayan aiki da kudi za mu rika fitar da kayayyakin da muke yi zuwa wasu kasashe.

Mene ne burinka?

Babban burina a wannan aiki shi ne in samu babban jari mu samu motar aiki da za mu rika sayo karafa daga Kano ko wasu wurare daban- daban. Kuma mu samu injin kankare karfe domin aikin ya rika yi mana sauri.