✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma ba sa son biyan bashi – Babban Bankin Najeriya

Ba kin biyan bashi ba ne, lokaci ne ya kure – Shugaban Manoman Shinkafa   An yi kira ga manoma da su rika biyan bashin…

Ba kin biyan bashi ba ne, lokaci ne ya kure – Shugaban Manoman Shinkafa

 

An yi kira ga manoma da su rika biyan bashin da suka karba daga bankuna don ci gaban harkar noma a kasar nan. Wanann kira ya fito ne daga bakin Daraktan Bangaren Kula da Maoma na Babban Banki, Muhammad Ali Abubakar, a lokacin da yake gabatar da takarda a wajen taron zauren tattaunawar manoman Arewa maso Yamma, wanda Kamfanin Daily Trust tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Noma ta Jihar Kano suka shirya.

Muhamamd Ali ya bayyana cewa tun daga lokacin da bababn bankin Najeriya (CBN) ya raba bashin kayan noma ga manoma har zuwa yanzu da suka yi girbi, bankin bai kaibi ko kashi 10 cikin 100 na bashin da ya ba su ba. “Kamar misali a Sakkwato mun bada bashi ga manoman alkama wadda muka sami labain bayan an yi girbi sun sayar da amfanin gonarsu akan Naira miliyan 250, amma abin mamaki ba su mayar da Naira miliyan 50 ga bankin ba.”

Darkatan ya kuma bayyana cewa idan har ana so harkar noma ta bunkasa, to dole ne sai manoma sun dauki aniyar biyan bashin dake kansu don bababn bankin ya ji dadin ci gaba da bayar da bashin ga sauran manoma. Har ila yau ya yi kira ga manoma da su jure wajen cika duk wasu ka’idoji da bankin ya shimfida wajen karbar bashin.

“Mun kula cewa mutanenmu na Arewa ba su da juriya wajen bin ka’idojin karbar bashin, wanda hakan ya janyo takwarorinmu na Kudu suka yi mana nisa a harkokin ci gaba daban-daban.”     

Sai dai a jawabinsa Shugaban manoman shinkafa na Jihar Kano, Alhaji Abubakar Haruna ya bayyana cewa ba wai manoman sun ki biyan bashin ne da ganagan ba, illa lokacin da manoma suka karbi bashin damina ta ja baya. A cewarsa lokacin da manoman suka karbi bashin lokaci ya riga ya kure, domin a lokacin ruwan sama daya kacal aka yi damina ta tsaya, hakan ya sa manoman suka tsaya da noma suka jira har sai lokacin noman rani.

“Ganin cewa damina ta tsaya bayan karbar bashin, sai manoma suka jira zuwa lokacin noman rani. A yanzu haka suna kan girbe amfaninsu wanda kuma da zarar sun kammala za su biya bashin da suka karba”

 

Sai kuma ya yi kira ga gwamnati da ta shirya wasu tarurrukan wayar da kai ga manoma don su kara fahimtar harkar karba tare da mayar da bashin gaba daya, kasancewar akwai karancin fahimtar lamarin a tattare da manoman.