✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma 7 sun rasu a hatsarin mota a Minna

FRSC ta tabbatar da faruwar hatsarin.

Wani mummunan hatsarin mota da ya auku da safiyar ranar Laraba a ƙauyen Panti, a kusa Minna, wanda ya yi sanadin mutuwar manoma bakwai.

Shaidu sun bayyana cewa direban wata mota ƙirar Toyota Corolla mai lamba ANW-243-AH, ya yi yunƙurin wuce wata babbar mota marar lamba, lamarin da ya jawo hatsarin.

“Ina kan babur dina ina tafiya a kan hanyar Kutigi, sai na ga hatsarin ya auku a gabana,” in ji wani mai suna Muhammad Hassan.

Ya ce, “Motar Corolla ɗin cike take da kayan abinci, kuma yayin da direban ya yi sa’ar wuce wata farar babbar mota, bai lura da wata tirela da aka ajiye a gefen hanya ba. Nan take ya yi karo da tirelar.”

Hassan ya ƙara da cewa manoman da suka rasa rayukansu sun fito ne daga ƙauyen Dasun, inda suka koma yankin saboda matsalar tsaro a Gabashin Neja.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da aukuwar hatsarin.

Ta bayyana cewa motar Corolla na kan hanyarta daga Batiti zuwa Kutigi, yayin da babbar motar ke tahowa daga Legas zuwa Abuja lokacin da hatsarin ya faru.