✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta shirya yin cefane a watan Janairu

Ganin yadda kulob din Manchester United da ke Ingila yake tangal-tangal a gasar rukunin Premier na Ingila a halin yanzu ta sa kulob din yanke…

Ganin yadda kulob din Manchester United da ke Ingila yake tangal-tangal a gasar rukunin Premier na Ingila a halin yanzu ta sa kulob din yanke shawarar cefano zaratan ’yan kwallo a watan Janairun 2014 inda aka sake bude kakar saye da sayar da ‘yan kwallo.
Daga cikin ’yan kwallon da kulob din yake tunanin zawarcinsu akwai dan kwallon tsakiya a kulob din Bayer Leberkusen da ke Jamus mai suna Lars Bender.
Rahotanni sun nuna tun da kulob din bai kashe kudi sosai a kakar saye da sayar da ’yan wasa da ta wuce ba, bayan ya sayo dan kwallon Eberton, Marouane Fellaini akan Fam miliyan 27 babu wani dan kwallon da kulob din ya sake saya har aka rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo.
Jaridar Daily Star da ke Ingila ta kalato cewa daga cikin ’yan kwallon da kulob din yake hankoron sayo su a watan Janairun badi akwai dan kwallon baya a kulob din Eberton mai suna Leighton Baines da kuma dan kwallon Atletico Bilbao da ke Sifen mai suna Ander Herrera.
Sai dai tuni Manajan kulob din Bayer Leberkusen  da ke Jamus, Micheal Reschke ya karyata sayar da dan kwallonsa Lars Bender ga kulob din United  a watan Janairun shekara mai zuwa.
Ya zuwa wannan lokaci Manchester United ta barar da wasanni uku daga cikin wasanni shida da ta yi a gasar rukunin Premier.