Idan da za a zo ai zaben gwanina,to ni dai ba ni da gwana ta gwanaye a shekarar 2015 sai Aisha Jummai Alhasan (Maman Taraba). Ita ce yanzu ta zama dan turmin dakan tsakar gida sha luguden mahassada, ita ko hassada Hausawa na cewa, ‘ga mai rabo taki ce.’
Lallai a tarihin siyasa, akwai mata da yawa a Najeriya, da suka taka rawa, suka kuma cancanci a kira su ‘abin koyi,’ kama daga Amina Sarauniyar Zazzau, zuwa irin su Gambo Sawaba da Sarah Jibril, kai har ma a wannan jamhuriya ba za a manta da Patricia Olubunmi Etteh da Misis Pauline Talllen da Salmot M. Badaru da Sarah Bisi Sosan da sauran su, duk mata ne da suka shiga cikin duniyar siyasa, suka taka rawa, duk da shingen kaya da buraguzai da aka gitta masu, amma suka tsallake, suka haye gashi. Yanzu sunayensu sun shiga kundin tarihi.
To, amma Aisha Jummai Alhasan ta bambanta da su . Saboda ko a shekarar 2011 da ta tsaya takarar Senata, an ce da gangan aka bata tikitin jam’iyyar, domin wanda zai kasance abokin takararta, wato Rabaran Jolly Nyame, ya samu saukin lashe zabe. Ashe ko an yi kuskure, domin sun manta da cewa, ba kowace mace take kanwar lasa ba. Gogewa da zuciya ta sa ranar 9 ga watan Afirilun 2011, ta kwada Jolly Nyame da kasa, kazalika ta maka Senata mai ci da kasa, inda ta kamfaci kuri’a mafi rinjaye har dubu114 da 131. Don haka dole Hukumar Zabe Mai zaman kanta INEC) ta bayyana ta, a matsayin wadda ta lashe zaben.
Duk da cewa, ita mace ce, ta kada bajimin dan siyasa a jihar da kabilanci da addini ke taka rawa. Masu fashin bakin siyasa na ganin kyautar ta kamar Sardauna da fara’arta da haba-haba da jama’a ba tare da la’akari da jinsi ko kabila ko ma addini ba, ya sa take da farin jini wajen ‘yan Taraba.
Lallai da jam’iyyar PDP a zaben 2015 ta san APC za ta tsayar da Jummai, to da sun yi shiri na musamman, da duk wannan kamuya-uyar kokarin kwace kujerar ta hanyar kotu a bai wa wanda ba shi ne mutanen Taraba ke so ba.
Saidai abin takaici, jam’iyyar PDP a Taraba kullum wayonta daya, kuma hanya daya take bi wajen shirya magudin zabe, wato amfani da addini da kabilanci. A iya lissafin ‘yan PDP a Taraba, shi ne, babu ta yadda za a yi mutanen Taraba su zabi mace, Musulma, Hausa-Fulani a matsayin gwamna ba. Wannan shi ne, kalaman da wasu ‘yan siyasar addini da kabilanci ke yi a Jihar Taraba, cewa, Musulmi ko Hausa-Fulani ba zai taba yin gwamna ba. Wannan ya sa lokacin da tsohon Gwamna danbaba danfulani Suntai ya hau jirgin sama ya fado, kuma matamaikinshi Alhaji Garba UTC ya zama mukaddashin gwamnan jihar, masu bakar wannan siyasa ta rarraba kawunan ‘ya’yan Jihar Taraba suka rikice, suka dimauce, suka rinka tada husuma da fitina, musamman a yankin Wukari. Kuma kowa ya sani cewa, suna yin haka ne, don ba su son addini da kabilar wanda Allah ya nufa ya jagorance su ba. Kazalika abin da ya faru ke nan lokacin da kotun sauraran karar zabe ta soke zaben jihar, ta bai wa Aisha Jummai; saboda kowa ya sani cewa, Darius Ishaku bai tsaya zaben fidda gwani na jam’iyya ba, amma saboda PDP ta yi kaurin suna wurin cin fuskar dimokuradiyya, abin da ya sa ma ke nan ta sha kasa a zaben shugaban kasa na 2015.
Abin da ya ba su tsoro, shi ne, duk da satar kuri’a da kwacewa da cika akwatuna da amfani da coci wajen yakar Jummai da amfani da farfagandar cewa, bai kamata a zabi mace gwamna a Jihar Taraba ba, sai ga shi hakan bai tsinana musu komai ba.
Yanzu dai kallo ya koma sama, ‘shaho ya dau giwa.’ Kotun koli ce kawai za ta iya canza wannan tarihi. Shin kotun nan za ta yi adalci ta bai wa Jummai kujerarta ko kuwa za ta bi ajandar ‘yan raba kai ta tabbatar wa Darius haramtacciyar kujerar ? Lokaci ne kawai zai nuna.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa 08165270879 [email protected].
Maman Taraba: Gwanar shekarar 2015
Idan da za a zo ai zaben gwanina,to ni dai ba ni da gwana ta gwanaye a shekarar 2015 sai Aisha Jummai Alhasan (Maman Taraba).…